Yanzu-yanzu: An samu karin mutane biyu da suka kamu da Coronavirus a Kano

Yanzu-yanzu: An samu karin mutane biyu da suka kamu da Coronavirus a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa an samu karin mutane biyu da suka kamu da cutar a jihar, kwana biyu da bullar cutar a jihar.

Hadimin gwamna Abdullahi Ganduje kan kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan ne da yammacin Litinin.

A yanzu , adadin mutanen da ke dauke da cutar a Kano ya zama uku.

Jawabin yace: "An sake samun mutum 2 da suka kamu da cutar Corona wato Covid-19 a jihar Kano, bayan sakamakon gwajin da akayi musu wanda ya tabbatar da cewa suna da cutar, wanda ya kawo adadin masu ita a Kano suka zama 3."

Mun kawo muku ranar Asabar cewa mutumin ya yi tafiya daga Legas zuwa Abuja sannan ya dira a Kano. An gwadashi ne a cibiyar gwajin dake asibitin koyarwan Aminu Kano AKTH.

Tuni an garzaya da shi dakin killace mutane a Kwanar Dawaki.

KU KARANTA An kama babban Limami, an kwace motoci 269 a Abuja

Yanzu-yanuz: An samu karin mutane biyu da suka kamu da Coronavirus a Kano

Coronavirus a Kano
Source: Facebook

A bangare guda, Jami'an hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC, sun shawarci tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya killace kansa bayan gwajin da akayi masa a jihar Kano.

Rahoton ya bayyana cewa hukumar NCDC ta ce hakan na cikin ka'idojin da aka kindaya ga mutanen da aka yiwa gwaji kafin sakamakon gwajinsu ya fito.

Sakamakon bibiyan mutanen da mutumin farko da ya kamu da cutar a Kano yayi mu'amala dasu, an gano cewa tsohon gwamna Lamido ya halarci wata jana'izar da mutumin ya halarta a Koki.

Shugaban ma'aikatar kiwon lafiyan jihar Kano, Dr. Imam Wada Bello, ya tura wasikar kar ta kwana ga Sule Lamido inda ya bukaci daukar jini da yawunsa domin gwaji.

Sule Lamido da kansa ya daura wasikar a shafinsa na Facebook inda aka bukaci gwada shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel