Yanzu-yanzu: Buhari ya ce mutan Abuja, Legas da Ogun su cigaba da zama a gida

Yanzu-yanzu: Buhari ya ce mutan Abuja, Legas da Ogun su cigaba da zama a gida

- Na kara tsawon ranakun dokar hana fita, Buhari ya sanar

- Ya ce za a kara yawan adadin wadanda ake bawa tallafin N5000 daga milyan 2.6 zuwa milyan 3.6

Shugaba Muhammadu Buhari ya kara umurtan mutan jihar Abuja, Legas da Ogun su kara zama a gida na tsawon makonni biyu domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yiwa yan Najeriya da yammacin Litinin, 13 ga watan Afrilu 2020.

Yace "Bayan kyakkyawan dubi cikin rahoton kwamitin ko-ta-kwana da shawarar da wasu suka bada, ya zama wajibi in kara ranakun hana fita a Legas, Ogun, da kuma birnin tarayya na tsawon kwanaki 14 fari daga 11:59 na daren Litinin, 13 ga Afrilu, 2020."

"Ina kara kira gareku ku baiwa gwamnati hadin kai wajen yakin nan."

"Wannan ba lamarin wasa bane, wannan lamarin mutuwa ko rai ne. An kulle Masallatai a Makkah da Madina. Fafaroma ya yi ista a coci babu jama'a."

"An kulle Indiya, Italiya da Faransa gaba daya. Hakazalika wasu kasashe sun bi sahu. Ba zai yiwu muyi jinkiri ba."

"Wannan shawara mai wuyar dauka ne amma ina da yaqinin cewa shine na kwarai. Hujjojin sun bayyana karara."

A wani labarin daban, Kwamitin tabbatar da biyayya ga umarnin zama a gida da hana taron jama'a a Abuja ya kama wani shugaban al'ummar Musulmi da ya sabawa matakin da hukuma ta dauka domin dakile yaduwar annobar cutar covid-19.

Shugaban kwamitin, Ikharo Attah, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja ranar Lahadi.

Ya kara da cewa, jami'an kwamitinsa sun kwace motoci 269 bayan samunsu da laifin sabawa umarnin a zauna a gida.

Yace "Mun fara aiki da sanyin safiyar yau (Lahadi) bayan wasu 'yan kasa nagari sun kiramu tare da sanar da mu cewa za a yi taron ibada a wata coci da ke unguwar Durumi. "

"Bayan mun isa Cocin sai muka iske cewa hakan ba gaskiya bane, amma mun sami Fasto a cikin Cocin tare da masu daukan hoton bidiyo."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel