Kyautan wutan lantarki na wata biyu: N109.8bn gwamnati zata kashe

Kyautan wutan lantarki na wata biyu: N109.8bn gwamnati zata kashe

Kudin da gwamnatin tarayya za ta kashe domin baiwa yan Najeriya kyautan wutan lantarki na tsawon watanni biyu da tayi alkawari zai kai akalla biliyan N109.8bn, lissafin Thisday ya bayyana

Zaku tuna cewa kakakin majalisar wakilan, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin yafewa yan Najeriya biyan kudin lantarkin watanni biyu sakamakon COVID-19.

Kungiyar kamfanonin rarrana wutan lantarki ANED, ta amince da wannan kudiri amma da sharadin cewa gwamnatin tarayya za ta biya kudin watanni biyun.

Lisaffin daga hukumar lura da wutan lantarki NERC da hukumar kasuwancin tilin wutan lantarki NBET ya nuna cewa sai gwamnati ta kashe akalla N109.8 billion.

Lissafin ya nuna cewa a watan Junairu 2019, kudin wutan da yan Najeriya ke ci na kaiwa tsakanin N53 billion da N55 billion.

Misali a 2019, mafi karancin kudin da aka kashe a wata shine a watan Yuni inda aka ci N47,583,048,273. 37. Mafi yawa kuwa a watan Disamba inda akaci N62,252,549,885.43.

A watan Junairun 2020 kuwa, an kashe N52,134,588,489.19.

KU KARANTA Ka killace kanka na tsawon kwanaki 14 - NCDC ta shawarci Sule Lamido

Kyautan wutan lantarki na wata biyu: N109.8bn gwamnati zata kashe

Kyautan wutan lantarki na wata biyu: N109.8bn gwamnati zata kashe
Source: Facebook

A bangare guda, Ministan wutan lantarki, Saleh Mamman, ya ce basu kammala tattaunawa da kamfanonin da ke rarraba wuta lantarki ba kan lamarin baiwa yan Najeriya wuta kyauta na tsawon wanni biyu.

Hakan ya biyo bayan jawabin kungiyar kamfanonin raba wutar lantarki a Najeriya (DisCos) inda suka ce gwamnatin tarayya zata biya kudin wutan da ake shirn baiwa jama'a kyauta.

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Juma'a inda yace idan gwamnati ta kammala tattaunawa, za a sanarwa yan Najeriya.

Ministan ya tabbatarwa yan Najerya cewa gwamnati na iyakan kokarinta wajen yaye halin radadin da annobar Coronavirus ta daurawa kasa.

Yace “Gwamnatin tarayya bata yanke shawara kan cewa za a baiwa yan Najeriya wutan lantarki kyauta na tsawon watanni biyu ba.“

“Idan mukayi hakan, za a sanar a hukumance.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel