Ka killace kanka na tsawon kwanaki 14 - NCDC ta shawarci Sule Lamido

Ka killace kanka na tsawon kwanaki 14 - NCDC ta shawarci Sule Lamido

Jami'an hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC, sun shawarci tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya killace kansa bayan gwajin da akayi masa a jihar Kano.

Rahoton ya bayyana cewa hukumar NCDC ta ce hakan na cikin ka'idojin da aka kindaya ga mutanen da aka yiwa gwaji kafin sakamakon gwajinsu ya fito.

Sakamakon bibiyan mutanen da mutumin farko da ya kamu cutar a Kano yayi mu'amala dasu, an gano cewa tsohon gwamna Lamido ya halarci wata jana'izar da mutumin ya halarta a Koki.

Shugaban ma'aikatar kiwon lafiyan jihar Kano, Dr. Imam Wada Bello, ya tura wasikar kar ta kwana ga Sule Lamido inda ya bukaci daukar jini da yawunsa domin gwaji.

Sule Lamido da kansa ya daura wasikar a shafinsa na Facebook inda ya aka bukaci gwada shi.

KU KARANTA Karya dokar ta-baci yasa za’a iya samun mutane 57,000 da zasu kamu da Corona a Kaduna

Ka killace kanka na tsawon kwanaki 14 - NCDC ta shawarci Sule Lamido

Ka killace kanka na tsawon kwanaki 14 - NCDC ta shawarci Sule Lamido
Source: Twitter

Wasikar tace “Assalamu Alaikum mai girma, daga cikin bibiyan da mukeyi na wadanda sukayi muamala da mai COVID-19, an ambaci sunanka cikin wadanda suka halarci jana'iza a Koki ranar Alhamis.“

“Muna neman izininka saboda jamian RRT su duba halin da kake ciki tare da daukan samfurinka.“

A martaninsa, Sule Lamido yace “Ba matsala, ina nan duk lokacin da kuke bukata na, ku sanar da ni lokacin.“

Daga baya tsohon gwamnan ya sake bayyana cewa “Kimanin karfe 1:30 na ranar 13/04/2020, Ni, direba na da dogari na mun yi dukkan gwaje-gwajen. Muna sauraron sakamako.”

A bangare guda, Kwamitin ko-ta-kwana dake yaki da yaduwar Coronavirus a jahar Kaduna ta bayyana yiwuwar samun ninkawar adadin masu dauke da cutar a jahar Kaduna saboda rashin bin doka.

Kwamitin ta ce sakamakon rashin yi ma dokar hana shige da fice biyayya, adadin masu dauke da cutar a jahar Kaduna za su iya kaiwa 57,000, idan dai ba an tabbatar da dabbaka dokar bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel