Karya dokar ta-baci yasa za’a iya samun mutane 57,000 da zasu kamu da Corona a Kaduna

Karya dokar ta-baci yasa za’a iya samun mutane 57,000 da zasu kamu da Corona a Kaduna

Kwamitin ko-ta-kwana dake yaki da yaduwar Coronavirus a jahar Kaduna ta bayyana yiwuwar samun ninkawar adadin masu dauke da cutar a jahar Kaduna saboda rashin bin doka.

Kwamitin ta ce sakamakon rashin yi ma dokar hana shige da fice biyayya, adadin masu dauke da cutar a jahar Kaduna za su iya kaiwa 57,000, idan dai ba an tabbatar da dabbaka dokar bane.

KU KARANTA: Mutane 5 sun sake kamuwa da annobar Coronavirus a Najeriya, jimilla 323

Gwamnatin ta damu ne bayan samun mutum na 6 dake dauke da cutar, wanda ya dawo daga jahar Legas, kuma motar haya ya bi, bayan an tabbatar da cutar a jikinsa ta hanyar gwaji.

Daga nan ne gwamnatin jahar ta fara dabbaka dokar da karfin tuwo domin tabbatar da jama’a sun zauna a gidajensu, tare da hana tafiye tafiye, har sai baba ta ji, domin hana yaduwar cutar.

Karya dokar ta-baci yasa za’a iya samun mutane 57,000 da zasu kamu da Corona a Kaduna

Jama'an Kaduna
Source: Twitter

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka inda ya jaddada bukatar jama’a su daina fita don kare kansu.

Aruwan yace sun umarci jami’an tsaro su mayar da duk wani matafiyi dake kokarin bi ta garin Kaduna, sai dai idan sun samu izinin ratsa garin ko kuma suna dauke da muhimman abubuwa.

Rahoton ta kara da cewa an kama motoci da dama a hanyar Kachia da Sabon Tasha, yayin da wasu direbobin suka saki motocinsu suka tsere don gudun kamen jami’an tsaro.

A wani labarin, Hukumar NCDC ta sanar da samun mutane 5 da suka kamu da annobar Coronavirus a Najeriya, wanda ya kawo adadin masu dauke da cutar zuwa 323.

Zuwa karfe 9:10 na daren Lahadi, akwai mutane 323 da aka tabbatar suna dauke da cutar COVID-19 da aka samu rahotonsu a Najeriya, 10 sun mutu, yayin da an sallami 85.

Jahohin da aka samu sabbin mutanen da suka kamu da cutar sun hada da jahar Legas, mutane biyu, jahar Kwara ita ma da mutane biyu sai kuma jahar Katsina inda mutum daya ya kamu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel