Iyalan mamaci 5 ko 6 kadai muka amince su yiwa gawa Sallar Jana'iza - Gwamnatin Saudiyya

Iyalan mamaci 5 ko 6 kadai muka amince su yiwa gawa Sallar Jana'iza - Gwamnatin Saudiyya

Gwamnatin kasar Saudiyya ta kindaya wasu ka'idoji ga iyalan dukkan wanda ya mutu sakamakon cutar Coronavirus saboda hana yaduwar cutar.

Masana kiwon lafiya da ilmin kwayoyin cututtuka sun bayyana cewa ana iya kamuwa da cutar ta Coronavirus daga cikin mutumin da ya mutu sakamakon cutar.

Haka ya sa an daina yiwa gawawwakin Musulmai wanka Jana'iza da ruwa; sai Taimama.

Ma'aikatar kiwon lafiyan kasa tace mutane biyar zuwa shida daga iyalan mamaci ne aka amince su gudanar da Sallar Jana'iza.

Yayinda ministan lamuran addinin Musulunci, Da’awah, da shiryar da a’umma na Saudiyya, Dr. Abdul Latif Al Sheikh, yake tsokaci kan hakan, ya ce Sallar Jana'iza bata na farilla muhimmanci ba.

Yace taruwar mutane a waje na iya rura yaduwar cutar cikin al“umma.

Yace “Wannan mataki ne da aka dauka na haramta taro na cewa a yi Sallolin Jana'iza a makabartu kuma kada iyalan mamacin sun wuce biyar ko shiga, sauran suyi sallarsu a gida.“

Iyalan mamaci 5 ko 6 kadai muka amince su yiwa gawa Sallar Jana'iza - Gwamnatin Saudiyya

Iyalan mamaci 5 ko 6 kadai muka amince su yiwa gawa Sallar Jana'iza
Source: Facebook

KU KARANTA Coronavirus: Babu Sallar Tarawihi bana - Kasar Saudiyya ta bayyana

A nan gida Najeriya, Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce gwamnati ba zata bayar da gawawwakin wadanda suka mutu sakamakon cutar Coronavirus ga iyalansu domin birnesu ba.

Ya ce ma'aikatar kiwon lafiya za ta birne saboda ana iya kamuwa da cutar daga cikin mamaci.

Ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi a taron kamfanin dillancin labarai NAN a Abuja.

A cewar NAN, ministan ya yabawa yan Najeriya bisa biyayyar da suka yiwa gwamnati kan dokar hana fita.

Yace: "Coronavirus cuta ce mai matukar hadari; har yanzu ba'a samu maganinta ba kuma ta nada ikon kisa, gajiyar da sashen kiwon lafiya da kuma karya tattalin arziki."

"A wasu kasashe cikin firji ake ajiye gawawwaki saboda dakunan ajiye gawawwaki sun cika. Yan Najeriya su sani cewa wannan ba irin gawawwakin da za'a basu bane su birne saboda hakkin ma'aikatar kiwon lafiya ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel