Coronavirus:An sallami 15 amma an samu karin mutane 5 da suka kamu a Najeriya

Coronavirus:An sallami 15 amma an samu karin mutane 5 da suka kamu a Najeriya

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya ta sanar da cewa an samu karin mutane biyar da suka kamu da cutar Coronavirus a fadin tarayya da kuma karin 15 suka samu waraka ranar Lahadi.

A jawabin da hukumar ta saki a daren Lahadi, ta ce an samu biyu a Legas, biyu a Kwara da daya a Katsina.

Jimillan adadin wadanda suka kamu yanzu a Najeriya 323. Daga cikin 85 sun warke kuma an sallamesu.

An samu bullar cutar a jihohi 19 a Najeriya.

A fadin duniya kuwa, mutane 1.7m sun kamu da cutar yayinda akalla 100,000 sun mutu.

Jihar Legas ce ke kan gaba da mutane 176, sai birnin tarayya Abuja mai mutane 56. Jihohin Benue, Neja, da Kano ne marasa mutane da yawa da suka kamu da COVID-19.

Coronavirus An sallami 15 amma an samu karin mutane 5 da suka kamu a Najeriya

Coronavirus Najeriya
Source: Facebook

KU KARANTA Sultan ya bayyana bacin rai da yadda gwamnoni suka bude wuraren ibada

Ga jerin jihohin

Lagos- 176

FCT- 56

Osun- 20

Edo- 12

Oyo- 11

Ogun- 7

Bauchi- 6

Kaduna- 6

Akwa Ibom- 5

Katsina-5

Kwara- 4

Delta- 3

Enugu- 2

Ekiti- 2

Rivers-2

Ondo- 2

Benue- 1

Niger- 1

Anambra- 1

Kano-1

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel