An kashe mutane da yawa, an kona gidaje da dama a rikicin kabilanci daya barke a Taraba

An kashe mutane da yawa, an kona gidaje da dama a rikicin kabilanci daya barke a Taraba

Wani sabon rikicin kabilanci ya barke a jahar Taraba tsakanin kabilun Shomo da Jole dake karamar hukumar Lau ta jahar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Daily Trust ta ruwaito a sanadiyyar rikicin, an kona garin Shomo Sarki gaba daya, inda a nan ne aka fi samun asarar rayuka da dukiyoyi.

KU KARANTA: Mutane 5 sun sake kamuwa da annobar Coronavirus a Najeriya, jimilla 323

An kashe mutane da yawa, an kona gidaje da dama a rikicin kabilanci daya barke a Taraba

Gwamnan Taraba
Source: Twitter

Rikicin ya samo asali ne a kan mallakin wani fadamar kamun kifi dake kusa da tafkin Benuwe, inda kabilun biyu suke zama, sakamakon tafkin ya ratsa ta cikin karamar hukumar Lau.

Yawaitan samun fadace fadace tsakaninsu ne tasa gwamnatin jahar a baya ta dakatar da dukkaninsu daga amfani da fadamar wajen kamun kifi.

Amma a wannan karo, jama’an guda daga cikin kabilun ne suka yi kokarin shiga fadamar don kamun kifi, yayin da jama’an dayar kabilar ta hanata da karfin tuwo, daga nan rikici ya kaure.

Daruruwan mutane da suka hada da mata, tsofaffi da kananan yara sun tsere daga gidajensu, kamar yadda shaidun gani da ido suka tabbatar.

Shi ma Kaakakin Yansandan jahar, David Misal ya tabbatar da aukuwar lamarin, yace tuni rundunar ta tura mataimakin kwamshinan Yansanda don tabbatar da zaman lafiya a yankin.

“Mun samu labarin rikicin, kuma ya shafi mutane da dama, amma ba zamu iya fadin adadin wadanda aka kashe ba, amma mataimakin kwamishinan Yansanda ya isa garin don dawo da zaman lafiya.” Inji shi.

A wani labarin kuma, miyagu sun yi garkuwa da wani yaro dan shekara 15, Abubakar Sadiq a jahar Bauchi, inda daga bisani suka halaka shi bayan amsan kudin fansa naira miliyan 4.5.

Premium Times ta ruwaito mahaifinsa, Rilwanu Abubakar, wanda likita ne a asibitin koyarwa ta jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ya bayyana cewa a kofar gidansu aka sace Abubakar.

Rilwanu yace yana wajen aiki aka sanar da shi lamarin, nan da nan kuma ya sanar da ofishin yan kato da gora dake yankinsu a garin Ningi, da kuma rundunar Yansandan jahar Bauchi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel