Hankula sun tashi yayinda aka nemi mai Coronavirus aka rasa a Anambara

Hankula sun tashi yayinda aka nemi mai Coronavirus aka rasa a Anambara

An samu tashin hankali a jihar Anambara yayinda aka nemi mutumin farko da ya kamu da cutar Coronavirus a jihar aka rasa.

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar ranar Juma'a cewa an tabbatar da bullar cutar ta COVID-19 a jihar.

Tun lokacin, al'ummar jihar sun kidime bayan samun labarin cewa mutumin ya ziyarci asibitoci daban-daban uku a jihar.

Hakazalika ya yi mu'amala da mutane da dama kafin arcewa.

Amma kwamishanan kiwon lafiya na jihar Anambara, Dakta Vincent Okpala, da kwamishanan yada labarai, C Don Adinuba, sun ce mutane su kwantar da hankulansu.

Sakamakon haka, gwamnan jihar, Willie Obiano, ya sanar da cewa a kulle jihar gaba daya ba tare da bata lokaci ba, a cewar rahoton The Nation.

Dokar hana fitan za ta fara aiki ne ranar Litinin inda za a fara da dukkan tashohin mota.

KU KARANTA Dokar hana walwala: An damke dan sanda ya karba cin hancin N40,000

Hankula sun tashi yayinda aka nemi mai Coronavirus aka rasa a Anambara

Hankula sun tashi yayinda aka nemi mai Coronavirus aka rasa a Anambara
Source: Depositphotos

KU KARANTA Shugaban kasar Chadi ya caccaki gwamnatin Najeriya a kan sakin 'yan Boko Haram

A jawabin hukumar yan sandan jihar ranar Lahadi, kakakin hukumar, Mohammed Haruna, ya bayyana cewa shirye suke da aiwatar da umurnin hana shiga da fita a jihar.

Ya ce mutumin ya shigo jihar Anambara tun ranar 28 ga Maris kuma da yiwuwan ya gogawa mutane da dama.

Jawabin yace: “Hukumar yan sandan jihar Anambara na sanarwa daukacin alummar jihar cewa bisa ga umurnin gwamnatin jihar domin takaita yaduwar cutar Coronavirus, an kaddamar da hana shiga da fita a jihar.“

“Saboda haka ana kira ga jamaa suyi zamansu a gida. Babu fita, babu zuwa unguwa.“

“An dauki wannan mataki ne domin gano mutumin tare da wadanda yayi mu'amala dasu domin hana yaduwar cutar.“

Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje ta ce za ta rufe wasu daga cikin kasuwannin da ke jihar tare da tsananta dokar hana shiga da fice a kan iyakokinta.

Hakan kuwa ya faru ne sakamakon bullar muguwar cutar coronavirus a jihar a ranar Asabar.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya shaidawa BBC cewa tuni aka killace wanda aka samu da cutar a asibitin Pfizer na kwanar Dawaki.

Dan shekaru 75 din da haihuwa na nan a killace don hana yaduwar cutar a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel