ASUU ta caccaki Buhari a kan shirin rage kasafin kudin ilimi da lafiya

ASUU ta caccaki Buhari a kan shirin rage kasafin kudin ilimi da lafiya

Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta gargadi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kan shirin rage kasafin kudin bangaren ilimi da na lafiya a kokarin da yake yi na rage kasafin kudin shekarar 2020.

ASUU ta sake jan kunnen gwamnati a kan damfarar 'yan Najeriya ta hanyar cakuda kudin da aka ware don shirin bayar da tallafi da kudaden gudunmawa da aka samu domin rabawa talakawa yayin da aka hana fita saboda annobar covid-19.

A cikin wani jawabi da ta fitar ranar Lahadi, ASUU ta ce ko kadan bai kamata gwamnati ta yi tunanin rage kasafin kudin bangaren ilimi da na lafiya ba.

Sanarwar, mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar ASUU reshen jami'ar Ibadan, Farfesa Ayo Akinwole, ta bayyana cewa gwamnati ba ta koyi wani darasi daga annobar cutar covid-19 ba, wacce ta tona koma bayan Najeriya a bangaren lafiya da ilimi.

ASUU ta caccaki Buhari a kan shirin rage kasafin kudin ilimi da lafiya
Ziyarar ASUU ga Buhari
Asali: Facebook

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin zabtare biliyan N50.76 daga kasafin biliyan N111.78 da aka warewa hukumar ilimin bai daya (UBEC) tare da sake zabtare biliyan N26.51 daga biliyan N44.49 da aka warewa bangaren lafiya a matakin farko a cikin kasafin kudin 2020.

DUBA WANNAN: 'Na ji jiki', Kauran Bauchi ya bayyana halin da ya shiga a cibiyar killacewa bayan ya kamu da covid-19

Akinwole ya bayyana cewa gwamnatin da ta san ciwo kanta ba za ta ware makudan kudi don kawai yi wa gini kwaskwarima ko sayen motoci ga bangarori ma su muhimmanci kamar ilimi da lafiya ba.

Kazalika, ya caccaki shirin bayar da tallafi na gwamnatin gwamnatin tarayya, wanda ya bayyana cewa akwai babbar alamar tambaya a kan shirin. Ya ce ba a bayar da tallafin ga wadanda ya dace.

Ya shawarci gwamnati ta nemi talakawa na gaske a cikin kauyuka domin ba su tallafin rage radadin zaman gida saboda annobar cutar covid-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng