Gobara ta lashe gidan man Aliko da ke Kano (Bidiyo)

Gobara ta lashe gidan man Aliko da ke Kano (Bidiyo)

- Gobara ta lashe gidan man Aliko da ke kan titin Maiduguri a birnin Kano

- Wani ganau ba jiyau ba ya ce gobarar ta fara ne wajen karfe 12 na tsakar daren Asabar

- Manyan motocin kashe gobara shida tare da mutane nagari suka taimaka aka kashe wutar da ta dauka sa'a daya

Gobara ta lashe gidan man Aliko da ke kan titin Maiduguri a birnin Kano.

Wani ganau ba jiyau ba, ya sanar da jaridar Solacebase cewa gobarar ta fara ne wajen karfe 12 na tsakar daren Juma'a.

Ta faru ne yayin da ake sauke mai daga tankoki a gidan man.

Ganau din ya ce tankoki biyu ne a cikin gidan man amma daya ce ke sauke man fetur din yayin da gobarar ta fara.

Dayan direban tankar ya hanzarta yin dabarar ficewa daga gidan man da gaggawa bayan ya ga dayar tankar ta kama da wuta.

Manyan motocin kashe gobara shida tare da mutane nagari ne suka taimaka aka kashe wutar da ta dauka sa'a daya.

Jaridar Solacebase ta gano cewa, gobarar ta tada hankulan jama'a da ke da gidaje kusa da gidan man da ke yankin Taraunin.

Da yawa daga cikinsu sun gaggauta barin gidajensu don tseratar da rayukansu.

KU KARANTA: Zamfara: Rundunar 'yan sandan ta samu kwaryar jini a gidan matsafi

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta gano kwarya mai cike da jini a gidan wani da ake zargi da zama dan kungiyar asiri a Gusau, babban birnin jihar.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, Mohammed Shehu ya bayyana wa manema labarai a ranar Asabar.

A makon da ya gabata ne Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa gidan 'yan kungiyar asirin na nan a kwatas din Dallatu da ke kusa da sabuwar tashar mita a Gusau.

'Yan sandan sun kai samame ne sakamakon ayyukan laifin da aka gano ana aikatawa a gidan.

Ya ce wadanda suka kai bayanan sun ce mazauna yankin sun gano cewa duk lokacin da matsafan suka shiga gidan, dukkan kananan halittu kamar sh kadangaru da kiyashi na mutuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel