Shugaban kasar Chadi ya caccaki gwamnatin Najeriya a kan sakin 'yan Boko Haram (Bidiyo)

Shugaban kasar Chadi ya caccaki gwamnatin Najeriya a kan sakin 'yan Boko Haram (Bidiyo)

- Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby ya umarci sojojin kasarsa da kada su kuskura su bar 'yan uwansu sojojin Najeriya su saki mayakan ta'addanci na Boko Haram

- A wani bidiyon da ya bazu a yanar gizo, an ga Deby yana sanar da sojojin cewa idan suka saki 'yan ta'addan, akwai yuwuwar su koma kasar Chadi tare da yin barna mai yawa

- A 2016, rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da Operation Safe Corridor don gyaran hali ga tubabbun 'yan Boko Haram, lamarin da sojojin suka soka

Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby ya umarci sojojin kasarsa da kada su kuskura su bar 'yan uwansu sojojin Najeriya su saki mayakan ta'addanci na Boko Haram.

A makon da ya gabata ne Rundunar sojin Chadin suka kai mummunan hari ga mayakan ta'addancin a yankin Goje-Chadi da ke dajin Sambisa, jaridar The Cable ta ruwaito.

Waje ne kuwa da mayakan ta'addancin suka yi katutu.

Dakarun sojin kasar Chadin, sun halaka mayakan ta'addancin masu tarin yawa sannan suka kwace makamai masu yawa daga wajensu.

A wani bidiyon da ya bazu a yanar gizo, an ga Deby yana sanar da sojojin cewa idan suka saki 'yan ta'addan, akwai yuwuwar su koma kasar Chadi tare da yin barna mai yawa.

"Wannan wurin ne zai zama mazauninku har sai Najeriya ta turo dakarunta. Ku zauna da su na wata daya. Kada su sakesu ko wani makaminsu, za su shigo Chadi ne," yace.

DUBA WANNAN: Na kama mijina yana cin amana ta har su biyu - Matar tsohon gwamnan APC

Ya kara da cewa, "Toh ya kamata su gane. Ba za mu bar lamarin haka ba. Nan da kwanaki kadan, zan yi magana da shugaban kasar Nijeriya".

"Kun halaka a kalla kashi 90 na Boko Haram. Wannan na tabbatar kuma zan iya sanar da duniya cewa an gama da kashi 90 na Boko Haram," a cewarsa.

Kamar yadda yace, "Ragowar kashi 10 kuwa suna nan suna yawo a cikin gari. Wasu sun tsere zuwa kasashen Nijar da Najeriya, amma ba za su taba dawowa Chadi ba. Chadi ba wurin Boko Haram bane."

A watan Maris din 2015, Deby ya ce Najeriya ba ta yakar Boko Haram.

A 2016, rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da Operation Safe Corridor don gyaran hali ga tubabbun 'yan Boko Haram, lamarin da sojojin suka soka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel