Yanzu-yanzu: An sallami mutum 10 da suka warke daga coronavirus a Osun

Yanzu-yanzu: An sallami mutum 10 da suka warke daga coronavirus a Osun

- Oyetola ya ce an sallami mutum 10 da suka warke daga coronavirus a jiharsa

- Gwamnan na Osun ya ce an yi wa mutanen gwaji har sau biyu kuma sakamakon ya nuna sun warke

- Majinyatan da suka warke suna cikin mutum 17 da suka dawo daga kasar Ivory Coast kuma aka gano sun kamu da cutar.

Wasu mutane 10 da suka kamu da cutar coronavirus a jihar Osun sun warke kuma an sallame su sun koma gidajensu.

Gwamnan da ya bayyana hakan a Osogbo a ranar Asabar 11 ga watan Afrilun 2020.

Ya ce an yi wa majinyatan da aka sallama gwaji har sau biyu kuma sakamakon ya nuna sun warke kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kazalika, wani rahoto da gwamnatin jihar ta wallafa a shafin ta na Twitter ya ce majinyatan da aka sallama suna daga cikin mutum 17 ta aka tabbatar sun kamu da cutar bayan sun dawo daga Ivory Coast.

DUBA WANNAN: Masana kimiyya sun gano magunguna 6 da ka iya kashe coronavirus

Gwamnatin jihar ta ce sauran majinyatan suna samun kulawar da ta dace kana suna samun sauki kuma "ana fatan za a sallame su da izinin Allah".

Wani sashi na sakon ya ce, "Gwamnatin jihar Osun ta sallami mutum 1O cikin 17 da aka gano sun kamu da cutar bayan sun dawo daga Ivory Coast. An musu gwaji sau biyu kuma sakamakon ya nuna sun warke.

"Sauran majinyatan bakwai suna samun sauki kuma suma ana fatan da ikon Allah za a sallame su nan ba da dadewa ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel