Zamfara: Rundunar 'yan sandan ta samu kwaryar jini a gidan matsafi
- Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta gano kwarya mai cike da jini a gidan wani da ake zargi da zama dan kungiyar asiri a Gusau
- A makon da ya gabata ne Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa gidan 'yan kungiyar asirin na nan a kwatas din Dallatu
- A yayin samamen, 'yan sandan sun samu kayayyakin tsafin da suka hada da kwarya mai cike da jini sai kuma sunayen wasu manyan 'yan siyasar jihar a rubuce a wata takardar
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta gano kwarya mai cike da jini a gidan wani da ake zargi da zama dan kungiyar asiri a Gusau, babban birnin jihar.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, Mohammed Shehu ya bayyana wa manema labarai a ranar Asabar.
A makon da ya gabata ne Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa gidan 'yan kungiyar asirin na nan a kwatas din Dallatu da ke kusa da sabuwar tashar mita a Gusau.
'Yan sandan sun kai samame ne sakamakon ayyukan laifin da aka gano ana aikatawa a gidan.
Ya ce wadanda suka kai bayanan sun ce mazauna yankin sun gano cewa duk lokacin da matsafan suka shiga gidan, dukkan kananan halittu kamar sh kadangaru da kiyashi na mutuwa.

Asali: UGC
KU KARANTA: Boko Haram: Buratai ya koma Arewa maso gabas har sai ta'addanci ya kare
A yayin samamen, 'yan sandan sun samu kayayyakin tsafin da suka hada da kwarya mai cike da jini, sai kuma sunayen wasu manyan 'yan siyasar jihar a rubuce a wata takardar.
Shehu ya ce an dauka samfurin jinin da aka tarar a kwaryar don tantancewa a dakin bincike.
An gano cewa jinin dan Adam ne da ke rukunin O. Ya ce ana ci gaba da bincike a kan lamarin a halin yanzu.
Jami'in hulda da jama'ar ya ce, a halin yanzu dai an kama wasu wadanda ake zargi da hannu a ciki.
Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa za ta sanar da jama'a abinda bincike ya nuna, jaridar Daily Trust ta wallafa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng