COVID-19: An sallami mutum hudu da suka warke daga coronavirus a Abuja

COVID-19: An sallami mutum hudu da suka warke daga coronavirus a Abuja

An sallami mutane hudu da suka kamu da coronavirus a babban birnin tarayya Abuja bayan an musu magani sun kuma warke.

Hukumar babban birnin tarayya Abuja, FCTA, ce ta sanar da hakan cikin wani sako da ta wallafa a Twitter a ranar Asabar.

Sakon ya ce, "FCTA ta tabbatar da sallamar mutane hudu da suka kamu da COVID19, hakan na nufin jimillar wadanda suka warke a Abuja yanzu 11 a ranar 11 ga watan Afrilun 2O2O."

Hukumar ta FCTA ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin cigaba da dakile yaduwar cutar a babban birnin tarayyar ta Najeriya.

DUBA WANNAN Coronavirus: Fitattun 'yan Najeriya 6 da suka warke daga COVID-19 (Hotuna)

A wani rahoton, mun kawo muku cewa an gano wani dauke da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo, lamarin da ya tayar hankulan jama'a a yayin da ake fama da annobar coronavirus.

Cibiyar lafiya ta duniya, WHO, ta ce an tabbatar da samun mai cutar a wani birni mai suna Beni da ke gabashin jamhuriyar Congo.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, mai dauke da cutar ya mutu ne a safiyar Alhamis a asibiti bayan ya nuna alamun cutar na kwanaki masu yawa.

Tabbatar da samuwar cutar ya zama koma baya ga jamhuriyar Congo a yayin da take kokarin yakar cutar coronavirus.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta bayyana, an sanar da hakan ne a yau Juma'a bayan mutuwar mai cutar a ranar Alhamis.

Baya ga barkewar Ebola, jamhuriyar Congo na fama da annobar coronavirus, kyanda da kuma cutar amai da gudawa wacce ta kashe dubban yara.

Mutane 215 ne suka kamu da cutar coronavirus a kasar. Mutane 20 suka rasa rayukansu yayin da 13 suka warke daga cutar.

Cibiyar kiwon lafiya ta duniya ta bayyana Ebola a matsayin annoba tun bayan da cutar ta barke a 2019.

Ta taba biranen Goma da wasu kasashe masu makwabtaka. Har zuwa Juma'a, ba a samu wani wanda ya kamu da cutar ba tun daga ranar 17 ga watan Fabrairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel