Masana kimiyya sun gano magunguna 6 da ka iya kashe coronavirus

Masana kimiyya sun gano magunguna 6 da ka iya kashe coronavirus

Masana kimiyya sun ware wasu sinadarai shida daga cikin 1000 da suka yi bincike a kansu da nufin amfani da su wurin hada maganin COVID-19 wato coronavirus kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Binciken masanan da aka wallafa a mujjalar Journal Nature ta yi gwaji a kan ingancin magungunan da ake amince da su da wadanda ake ganin za su iya kashe kwayar cutar ta coronavirus.

Farfesa Luke Guddat daga Jamiar Queensland a Australia ya ce, "A halin yanzu babu takamamen magani ko hanyar warkar da wadanda suka kamu da kwayar cutar COVID-19."

Masana kimiyya sun gano magunguna 6 da ka iya kashe coronavirus

Masana kimiyya sun gano magunguna 6 da ka iya kashe coronavirus
Source: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Wani mutum ya mutu a Kano bayan ya killace kansa

"Domin gano sinadarin da za ayi amfani da su a asibitoci, mun fara wani shiri na musamman na gwajin magunguna a dakunan bincike da kuma amfani da manhajar kwamfuta domin yin kiyashin yadda magungunan za su yi yaki da kwayar cutar," in ji Guddat.

Masu binciken sun ce binciken ya fi mayar da hankali ne a kan muhimmin kwayar hallitar da ke taimakawa COVID-19 hayayyafa a cikin mutum mai suna protease ko Mpro.

"Hakan yasa zai dace ayi amfani da shi wurin hada maganin dakile kwayar cutar kuma mutane ba su da wannan sinadarin a jikinsu saboda haka akwai yiwuwar ba zai musu illa sosai ba," a cewar masu binciken.

Guddat ya ce, "mu kan gauraya magungunan a kan sinadarin hallitar ko kuma tsokar da muka saka kwayar cutar a kai sai mu duba ko maganin yana kashe kwayar cutar ko akasin haka.

"Idan har maganin kalilan yana iya kashe kwayar cutar toh akwai yiwuwar mu na kan hanyar samun maganin cutar idan an zurfafa bincike."

Bayan gwada dubban sinadarai, masu binciken sun gano cewa akwai magunguna shida da suka nuna alamun za su iya kashe kwayar cutar amma sun mayar da hankali a kan guda daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel