Boko Haram: Buratai ya koma Arewa maso gabas har sai ta'addanci ya kare

Boko Haram: Buratai ya koma Arewa maso gabas har sai ta'addanci ya kare

- Shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Buratai ya koma yankin Arewa maso gabas na kasar nan don jagorantar yakar Boko Haram

- Rundunar sojin Najeriya ce ta sanar da hakan a jiya Juma'a, 10 ga watan Afirilu

- Tun daga ranar 4 ga watan Afirilu ne Buratai ya je zagaya sojojin da ke yankin Arewa maso gabas din

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya koma yankin Arewa maso gabas din kasar nan don jagoràntar yaki da 'yan ta'adda.

Legit.ng ta ruwaito hakan ne bayan takardar da daraktan hulda da jama'a na rundunar, Kanal Sagir Musa, ta fita a ranar Juma'a, 10 ga watan Afirilu.

A yayin jawabi ga dakarun da ke sansanin Ngamdu da ke karamar hukumar Kaga ta jihar Borno, Buratai ya ce zai kasance tare dasu duk rintsi da tsanani.

Kamar yadda takardar ta bayyana, shugaban rundunar yana yankin Arewa maso gabas din tun a ranar 4 ga watan Afirilu don zagaya wuraren da dakarun suke.

Takardar ta kara bayyana cewa, a yayin zagayen, ya samu damar zantawa da manyan hafsoshin sojin tare da rundunoni.

Boko Haram: Buratai ya koma Arewa maso gabas har sai ta'addanci ya kare
Boko Haram: Buratai ya koma Arewa maso gabas har sai ta'addanci ya kare
Asali: Twitter

KU KARANTA: Muhimman abubuwa 2 da muka tattauna da shugaban kasa - Osinbajo

"Rundunar sojin Najeriya na shaidawa 'yan Najeriya cewa ta mayar da hankali wajen kare 'yan kasa tare da rayukansu.

"Akwai bukatar jama'a su san cewa babu wani kalubalen tsaro da ya gagara. Boko Haram da ISWAP sun kusa zama tarihi", takardar tace.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta dauka tsauraran matakai don ganin bayan mayakan Boko Haram.

Ya sanar da hakan ne a fadar shugaban kasa a Abuja yayin da ya karba bakuncin Gwamna Babagana Zulum na jihar Yobe a ranar Alhamis.

An yi taron ne bayan aikin da dakarun kasar Chadi suka yi a yankin tafkin Chadi bayan an halaka musu sojoji 100.

Buhari ya ce wadannan matakan sun zama dole a daukesu don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da ci gaba a yankunan da Boko Haram suka yada zango a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel