Hantarar 'yan Najeriya a China: 'Yan majalisa sun yi wa jakadan China kiran gaggawa

Hantarar 'yan Najeriya a China: 'Yan majalisa sun yi wa jakadan China kiran gaggawa

A taron da ya wanzu tsakanin kakakin majalisar tarayya, Femi Gbajabiamila da jakadan kasar China a Najeriya, Zhou Pingjian, kakakin ya bayyana cewa ya zama tilas a shawo kan cin zarafin da 'yan Najeriya ke fuskanta a kasar China da gaggawa.

Taron ya samu halartar shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu da mataimakin shugaban marasa rinjayen majalisar, Toby Okechukwu, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Kamar yadda takardar da mai bada shawara na musamman ga kakakin majalisar, Lanre Lasisi ya fitar, kakakin ya nuna bidiyon yadda jami'an kasar Chinan ke hantarar 'yan Najeriya.

Kakakin ya bayyana cewa, a bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta, an ga jami'an kasar Chinan suna korar 'yan Najeriya daga gidaje da kuma otal a kasar. Sun kara da kwace musu fasfotinsu.

Gbajabiamila ya kara da cewa, an sake killace 'yan Najeriya na kwanaki 14 bayan kammala kwanaki 14 da suka yi a killace.

Kakakin majalisar yace tabbas akwai bukatar samun bayani daga hukumomin a kan wannan lamarin.

"In har dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ana yinta ne don amfanin juna, toh dole ne a mutunta 'yan dukkan kasashen.

"A matsayinmu na gwamnati, ba za mu amince a ci zarafin 'yan kasar China ko wasu kasashen duniya ba a Najeriya.

Hantarar 'yan Najeriya a China: 'Yan majalisa sun yi wa jakadan China kiran gaggawa
Hantarar 'yan Najeriya a China: 'Yan majalisa sun yi wa jakadan China kiran gaggawa
Asali: UGC

KU KARANTA: Kisan dakarun Chadi: Buhari ya yi alkawarin daukar tsauraran matakai a kan Boko Haram

"Yadda kuke yi wa 'yan kasar, haka muke tsammanin za ku yi wa 'yan wasu kasashe. Ba za mu amince 'yan kasa na karya doka ba. Amma laifin dan kasa daya kuma bai dace ya shafi dukkan kasar ba," Gbajabiamila ya bayyana.

A martanin jakada Pingjian, ya ce duk da hukumar bata sanar da shi lamarin ba, zai gaggauta sanar da gwamnatin kasar.

"Mun dauka dangantakar da ke tsakaninmu da Najeriya mai matukar amfani. Har sai na samu rahoto daga gida, sannan zan dauka mataki. Amma ina tabbatar muku cewa ba doka bace.

"Mun dauka 'yan Najeriya daya da 'yan kasar mu, amma a yayin tabbatar da dokokin annobar, zai yuwu wasu al'amuran su faru. A yau zan sanar da hukumomin gida," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng