Ba a bamu komai ba - mazauna Abuja sun fasa kwai a kan ba su tallafi saboda annobar covid-19

Ba a bamu komai ba - mazauna Abuja sun fasa kwai a kan ba su tallafi saboda annobar covid-19

'Yan Najeriya, mazauna Abuja, da ya kamata su ci moriyar tsarin bayar da tallafi don rage radadi da matsin tattalin arziki da annobar cutar covid-19 ta haifar, sun musanta cewa an ba su tallafin kudi ko kuma na kaya daga wurin gwamnati.

Ministar walwala da jin dadin jama'a, Sadiya Umar Farouq, ta ce talakawan Najeriya da masu karamin karfi miliyan 2.6 sun ci moriyar shirin bayar da tallafi na gwamnatin tarayya.

Ta bayyana cewar kimanin gidaje miliyan 11 aka zaba tare da ba su tallafin kudi a jihohin Najeriya 35.

Ministar ta ce an zabi gidajen talakawa 5,982 da aka bawa talllafin a Abuja, gidajen talakawa 8,271 a jihar Nasarawa, 6,732 a jihar Katsina, da kuma jihar Anambra inda gidajen talakawa 1,367 suka ci moriyar shirin.

Amma duk da hakan, wani bincike da jaridar SaharaReporters ta yi ikirarin cewa ta gudanar a tsakanin talakawa da masu karamin karfi mazauna yankin Dutsen Alhaji, Kuje, Gwagwalada da Gudu a Abuja, ya gano cewa jama'a ba su da masaniyar an raba N20,000 a matsayin tallafi.

Ba a bamu komai ba - mazauna Abuja sun fasa kwai a kan ba su tallafi saboda annobar covid-19
Sadiya Farouq yayin rabon tallafin kudi ga talakwa a Abuja
Asali: Twitter

Mazauna unguwannin sun bayyana cewar ba su san an bayar da wani tallafin kudi domin rage wa talaka radadin matsin tattalin arziki da annobar cutar coronavirus ta haifar ba.

Tun a shekarar 2017 gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta karbi bayanan wasu talakawa da za ta ke bawa tallafin kudi, N5,000, kowanne wata a karkashin tsarin bayar da tallafi da tabbatar da jin dadi da walwalar jama'a.

DUBA WANNAN: Ngozi Okonjo-Nweala; Tsohuwar ministar PDP ta samu babban mukami a IMF

SaharaReporters ta ce bincikenta ya gano cewa gwamnati ba ta iya biyan masu cin moriyar shirin a kowanne watan Janairu tun shekarar 2017.

"Su na tsallake watan Janairu na kowacce shekara, sai a watan Fabrairu sannan su biya N10,000, kudin wata biyu, amma wannan shekarar hakan ma ba ta samu ba.

"Sai farkon watan Afrilu su ka fara biyan kudin a cikin shekarar nan. Sun biya N20,000 a dunkule (N5,000 kowanne wata daga Janairu). Ba su fada wa masu cin moriyar shirin cewa kudin da aka biya su tallafin rage radadin matsin tattalin arziki da annobar covid-19 ta kawo bane," a cewar majiyar SaharaReporters.

Mazauna yankunan Abuja da su ke da yawan talakawa sun bayyana matukar mamakinsu da kaduwa bayan sun samu labarin cewa gwamnatin tarayya ta na kwarmata cewa ta ba su tallafin N20,000 domin rage musu radadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel