Coronavirus: An sake sallamar mutum 3 da suka warke a Oyo

Coronavirus: An sake sallamar mutum 3 da suka warke a Oyo

- Mutane uku ne suka warke daga cutar coronavirus a jihar Oyo bayan jinyar da suka yi a cibiyar killace masu cututtukan da ke yaduwa

- Kamar yadda gwamnan jihar ya bayyana, jimillar wadanda suka warke daga cutar a jihar sun kai biyar

- Ya kara da cewa dokar ta-bacin da aka saka a jihar na nan daram amma banda ababen hawa masu dauke da abinci da magani

Mutane uku ne suka warke daga cutar coronavirus a jihar Oyo, jaridar The Nation ta wallafa.

An sallamesu daga cibiyar killace masu fama da cututtuka masu yaduwa bayan an gane sun warke sarai.

An damka su ga 'yan uwansu bayan gwaji kashi na biyu ya nuna sun warke daga cutar.

Wannan ne yasa jimillar wadanda aka sallama masu cutar a jihar suka kai biyar. Sauran shida ne ke asibiti suna jinya.

Gwamna Seyi Makinde, wanda ya ke jagorantar kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar Oyo, ya bayyana hakan ne yayin jawabi a kan kokarinsu na fatattakar cutar.

Amma kuma, Gwamnan ya sake jaddada haramcin taron sama da mutane 10 a jihar.

Ya ce dokar ta-bacin da aka saka a jihar har yanzu ba a dage ta ba.

Coronavirus: An sake sallamar mutum 3 da suka warke a Oyo
Coronavirus: An sake sallamar mutum 3 da suka warke a Oyo
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Biyu sun mutu, 17 su na kwance asibiti bayan cin abinci mai guba a gidan biki a Katsina

Gwamnan ya ce ababen hawa dauke da kayayyakin abinci, magunguna, kayayyakin asibiti da na man fetur ne kadai za a bari shiga jihar.

Makinda ya ce: "A jiya ne aka tabbatar da cewa majinyatan coronavirus uku sun warke sarai. Hakan ya kai ga yawan wadanda aka sallama suka kai biyar a jihar. A halin yanzu akwai mutane 6 da ke jinya".

Ya kara da cewa, "Dukkan matakan da muka dauka don hana yaduwar cutar a jihar na nan. Dokar ta-baci, hana taron mutane fiye da goma da kuma rufe kasuwanni banda na abinci".

Ya kara da rokon jama'ar jihar da su kiyaye da umarnin gwamnatin jihar.

Wanke hannu da ruwa, sabulu da kuma sinadarin kashe kwayoyin cutuka akai-akai duk mafita ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel