Da duminsa: An yi sulhu tsakanin hukumar tace fina-finai da Arewa24

Da duminsa: An yi sulhu tsakanin hukumar tace fina-finai da Arewa24

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Ismail Afakallah ta yi sulhu da gidan talabijin Arewa24 bayan takaddama da suka samu a farkon makon nan.

Cikin wata takardar sanarwa dauke da sa hannun sakataren hukumar, an samu matsaya tsakanin hukumar kan wasu fina-finai biyu da aka dakatad da haskasu.

Afakallahu ya yabawa shugabannin Arewa24 bisa dattakun da suka nuna wajen zaman sulhun.

Jawabin yace “Babban sakataren hukumar tace fina-finai ta jihar Kanom Alhaji Ismail Muhammad Na Abba Afakallah, yana mika godiyarsa ga Arewa24 bisa amincewar hadin kai da hukumar.“

“An yi yarjejeniya a zaman da mukayi cewa za a cire wuraren da ke nuna rashin tarbiyya a shirin Kwana Casa'in kafin a sake hasakata.“

“Hakazalika hukumar da Arewa24 sun amince da cewa sai hukumar ta tantance dukkan fina-finai da shirye-shirye kafin Arewa24 ta haskasu a tasharta.“

Da duminsa: An yi sulhu tsakanin hukumar tace fina-finai da Arewa24

Da duminsa: An yi sulhu tsakanin hukumar tace fina-finai da Arewa24
Source: Instagram

A bayan mun kawo muku rahoton cewa hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a karkashin shugabancin Isma'il Na'Abba Afakalla ta ba gidan talabijin mai zaman kanshi na Arewa 24 umarnin dakatar da haska fina-finan Kwana Casa'in da Gidan Badamasi.

Ta basu wa'adin sa'o'i 48 ne don tabbatar da an dena haska su saboda sun taka dokar jihar Kano.

Kamar yadda wani sashi na takardar da hukumar ta aika wa gidan talabijin din ta bayyana, ta ce ta dauka wannan matakin ne saboda wani sashi na fim din kwana casa'in din ya saba wa al'adar jama'ar jihar Kano.

Akwai wani sashi da aka nuna a shirin makon da ya gabata, inda aka nuna wani mutum ya rungumi wata a cikin wani kantin sayar da kaya na Sahad Stores da ke Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel