COVID-19: Jarrabawa ce Allah ya min - Bala Mohammed

COVID-19: Jarrabawa ce Allah ya min - Bala Mohammed

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya ce ya zama dole ya yi wa Allah godiya saboda jarrabawar da ya yi masa da kuma warkar da shi daga kwayar cutar COVID-19 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A jawabin da ya yi wa manema labarai a gidan gwamnati bayan an sallame shi, ya mika godiyarsa ga yan Najeriya da mutanen jiharsa musamman sarakuna, malamai da magoya bayansa bisa kauna da goyon baya da suka nuna masa lokacin yana killace.

Mohammed ya ce, "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah. Mun gode wa Allah bisa wannan jarrabawar. Ya zama dole in gode masa saboda jarrabawar da ya min da wannan kwayar cutar. Ina matukar gode muku.

COVID-19: Jarrabawa ce Allah ya min - Bala Mohammed

COVID-19: Jarrabawa ce Allah ya min - Bala Mohammed
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Na kama mijina yana cin amana ta har su biyu - Matar tsohon gwamnan APC

"Wannan cutar da ta kama ni mummunar cuta ce. Na gode wa Allah da ya warkar da ni. Ina neman afuwar duk wani matsala da na janyo wa kowa a Bauchi da ma Najeriya baki daya, ba nufi na bane kamuwa da cutar."

Gwamna Mohammed ya ce ya fahimci irin kauna da girmamawa da alummar jiharsa ke masa da iyalansa lokacin da ya kamu da cutar tare da cewa zai cigaba da dage wa domin ganin ya sauke nauyin alumma da ke kansa.

Gwamnan ya yi kira da magoya bayansa da sauran masu masa fatan alheri kada su damu kansu da zuwa gidan gwamnati domin gaishe shi, ya ce ya riga ya yi godiya bisa adduoin da suke masa.

Ya ce, "Ina kira ga mutane ba sai sun zo gidan gwamnati sun gaishe ni ba, na riga na gode bisa adduan da suka yi min, mu kiyaye dokar takaita cudanya tsakanin mutane da yawa da masana lafiya suka bayar."

Ya yaba wa kwamitin ko ta kwana na yaki da cutar coronavirus saboda ayyukan da suke yi kuma ya yi alkawarin ba su dukkan goyon bayan da suke bukata don cimma manufofin su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel