Da duminsa: An kafa cibiyar gwajin Coronavirus a Kano, ta farko a Arewacin Najeriya

Da duminsa: An kafa cibiyar gwajin Coronavirus a Kano, ta farko a Arewacin Najeriya

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta kammala kafa cibiyar gwajin cutar Coronavirus a asibitin koyarwar Malam Aminu Kano dake jihar Kano, ta farko a Arewa

Kafa wannan cibiyar cika alkawari ne da gwamnatin tarayya tayi na samar da dakin bincike na musamman domin gwajin cutar COVID-19 a Kano da wasu jihohin Arewa maso yamma.

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, wanda ya kai ziyarar ganin ido cibiyar a daren Alhamis ya bayyana cewa daga yanzu za a fara gwaji a Kano.

Yace: “Daga yanzu, ba za a sake kai samfurin jinin mutane Abuja ba domin gwaji. A Kano za a yi.“

“Mun zo yawon ganin ido domin tabbatar da abinda ke kasa ne, kuma bisa abinda muka gani a cikin dakin gwajin, an kammala shirya kayayyakin kuma an fara gwaji.“

Da duminsa: An kafa cibiyar gwajin Coronavirus a Kano, ta farko a Arewacin Najeriya
Gawuna Ganduje
Asali: Twitter

KU KARANTA Ban taba sanin halin da cibiyoyin lafiyar kasar nan ke ciki ya kazanta ba - Boss Mustapha

Ya mika godiyar gwamnatin jihar Kano karkashin gwaman Abdullahi Umar Ganduje, ga gwamnatin tarayya bisa wannan cibiya a Kano.

Gawuna ya ce sauran jihohi masu makwabtaka da Kano za su iya zuwa gwaji cibiyar.

Yayinda suke zagaye cikin cibiya, wani maaikacin NCDC, AbdulMaid Musa, ya ce babu irin gwain da ba za a iya ba a cibiyar.

Hakazalika an fara horar da maaikatan asibitin AKTH da gwamnatin jihar kan yadda zasu rika amfani da kayayyakin.

Shugaban asibitin AKTH, Farfesa Abdurrahaman Sheshe, ya yabawa jajircewan kwamitin yakar Coronavirus ta jihar karkashin jagorancin mataimakin gwamnan bisa yadda aka wayar da kan mutane kan matakan takaita yaduwar cutar.

Gabanin kafa wannan cibiya, babu wajen gwajin cutar Coronavirus ko daya a jihohin Arewacin Najeriya 19.

Birnin tarayya Abuja ake kai samfurin mutanen Arewa sannan a dawo da sakamakon.

Kano ta shiga sawun jihohi irinsu Legas, Edo, Osun, Oyo, da Abuja masu cibiyar gwajin cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel