Kisan dakarun Chadi: Buhari ya yi alkawarin daukar tsauraran matakai a kan Boko Haram

Kisan dakarun Chadi: Buhari ya yi alkawarin daukar tsauraran matakai a kan Boko Haram

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta dauka tsauraran matakai don ganin bayan mayakan Boko Haram.

Ya sanar da hakan ne a fadar shugaban kasa a Abuja yayin da ya karba bakuncin Gwamna Babagana Zulum na jihar Yobe a ranar Alhamis.

An yi taron ne bayan aikin da dakarun kasar Chadi suka yi a yankin tafkin Chadi bayan an halaka musu sojoji 100.

Buhari ya ce wadannan matakan sun zama dole a daukesu don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da ci gaba a yankunan da Boko Haram suka yada zango a Najeriya.

Zulum ya yi bayanin yadda sojojin kasar Chadin suka hari 'yan ta'addan da kuma abinda hakan zai iya jawowa tsaron kasar nan.

Zulum da Buhari sun amince da cewa yanzu lokaci yayi da za su kawo karshen wannan mummunan lamarin na Boko Haram da sauran miyagun lamurra da ke faruwa a yankin.

A yayin martani ga harin da dakarun kasar Chadi suka kai wa 'yan ta'addan, Zulum ya ce: "Sakamakon harin da suka kai wa 'yan ta'addan, sun fara tserowa daga yankin tafkin Chadi zuwa arewaci da kudancin jihar Borno. Akwai bukatar mu samar da hanyar halaka su da gaggawa".

Kisan dakarun Chadi: Buhari ya yi alkawarin daukar tsauraran matakai a kan Boko Haram
Kisan dakarun Chadi: Buhari ya yi alkawarin daukar tsauraran matakai a kan Boko Haram
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: An sake jaddada wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da Chadi

A jiya ne kasar Najeriya da jamhuriyar Chadi a ranar Alhamis sun amince da jaddada yarjejeniyar yakar Boko Haram da ke tsakaninsu.

Ministan tsaro, Manjo janar Bashir Magashi mai murabus ya sanar da hakan ne a taron da aka yi tsakanin hukumomin kasashen biyu a Abuja.

Ya ce yana farin cikin jaddada yarjejeniyar da ke tsakaninsu don ci gaba da tabbatar da nasarar jami'an tsaron hadin guiwa.

Ya ce kirkirar MNJTF da kasashen suka yi ya kawo babbar nasara wajen yaki da ta'addanci. Ya ce akwai bukatar su jaddada yarjejeniyar.

"Akwai bukatar mu nemi sabbin hanyoyin kawo karshen Boko Haram kuma wannan taron zai samar da amintattaun hanyoyin fatattakar ta'addancin.

"Muna bukatar sabbin tsare-tsare wajen kawo karshen ta'addanci in har muna son yankunanmu su zauna lafiya," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel