Ba mu bukatar ka a jamiyyar APC: Kungiya ta fada wa Matawalle

Ba mu bukatar ka a jamiyyar APC: Kungiya ta fada wa Matawalle

Wata kungiya mai suna The Concerned Citizens of Zamfara State ta bayyana cewa akwai yiwuwar jamiyyar APC ta rasa mambobi da magoya bayan ta masu yawa idan Gwamna Bello Matawalle ya shiga jamiyyar.

A cewar kungiyar, shigar gwamnan jamiyyar babban kuskure ne a siyasance inda ta yi ikirarin ba shi da cancanta da zai jagoranci mutane a harkar siyasa.

Sun yi wannan jawabin ne a matsayin martani kan rahoton cewa wasu manyan APC suna yi wa gwamnan matsin lamba cewa ya shigo jamiyyar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ba mu bukatar ka a jamiyyar APC, Kungiya ta fada wa Matawalle

Ba mu bukatar ka a jamiyyar APC, Kungiya ta fada wa Matawalle
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Na kama mijina yana cin amana ta har su biyu - Matar tsohon gwamnan APC

Sakataren kungiyar, Comrade Musa Gusau, ya ce mafi yawancin wadanda ke yi wa Matawalle matsin lamba ya shiga APC yan PDP ne.

Ya ce, "Eh, ko wane dan siyasa yana kokarin janyo mutane zuwa jamiyyarsa musamman gwamna amma ba irin su Matawalle ba wanda cikin watanni 11 da karbar mulki ya saka abubuwa sun tabarbare a jihar.

"Mutane sun yi amfani da kuriunsu sun nuna basu son shi yayi zabe kuma suna ta addua kada Allah ya bashi ikon koma wa APC domin su koya masa darasi irin na siyasa a zabe mai zuwa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel