An kashe masu yi wa 'yan bindiga leken asiri biyu a Katsina

An kashe masu yi wa 'yan bindiga leken asiri biyu a Katsina

An kashe wasu mutane biyu Ibrahim Maye da Bishir Mai Laya da ake zargin suna daga cikin manyan masu yi wa 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane leken asiri a Katsina.

An kashe mutane biyu ne a karshen makon da ya gabata a yayin da suke kokarin isar wa masu garkuwa da mutane sako a kusa da dajin Kasuwar Gora a karamar hukumar Safana.

Dukkansu biyun sun fito ne daga kauyen Hayin Gada a karamar hukumar Dutsinma na jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rahoto daga majiya ta ce da isar su dajin, sun hadu da wani tsohon dan leken asiri mai suna Amale amma ba su san cewa ya tuba ya rungumi shirin yin afuwa ga gwamnatin jihar ba.

An kashe masu yi wa 'yan bindiga leken asiri biyu a Katsina

An kashe masu yi wa 'yan bindiga leken asiri biyu a Katsina
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Na kama mijina yana cin amana ta har su biyu - Matar tsohon gwamnan APC

Duba da cewa ba su san ya dena sanaar ba, ya mika musu sunaye da hotunan mutane uku da za a yi garkuwa da su domin karbar kudin fansa.

Sunayen da aka bayar na yan kasuwa, Abu Farar Waina da wasu mata biyu an kirkire su ne kawai saboda a kama 'yan leken asirin amma babu mutane masu wannan sunan.

Daga baya an gano cewa wannan tarkon da aka kafa ya yi sanadin kama wasu manyan yan leken asiri da suka amsa cewa suna da hannu wurin sace jami'in kwastam, Nasiru da wasu 'yan biyu maza a kauyen Gizagawa.

Bayan sun tona asirin sauran 'yan leken asirin, an kashe mutanen biyu sannan aka aike da gawar su zuwa wani tubabben dan bindiga, Kachalla, wanda ya mika gawar ga jamian tsaro.

Majiya daga yan sanda ta ce tuni an fara farautar sauran 'yan leken asirin bakwai da aka ce suna aiki a kauyukan Dutsinma da Kagara.

Da aka tuntube shi, Kakakin 'yan sandan jihar, Gambo Isah ya yi alkawarin zai yi bincike a kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel