Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa wani tsohon sanata rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa wani tsohon sanata rasuwa

- Robert Koleoso, tsohon sanatan jihar Oyo ta Arewa tsakanin 2003 zuwa 2007 ya rasu

- Dan asalin karamar hukumar Saki ne ta jihar Oyo kuma ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Ibadan

- Dan uwan mamacin mai suna Adeniyi Adebisi ne ya tabbatar wa jaridar Premium Times mutuwar a daren Alhamis

Robert Koleoso, tsohon sanatan jihar Oyo ta Arewa tsakanin 2003 zuwa 2007 ya rasu.

Koleoso dan asalin karamar hukumar Saki ne ta jihar Oyo. Ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Ibadan, babban birnin jihar.

Mamacin dan uwan Michael Koleoso ne, tsohon sakataren gwamnatin jihar Oyo a zamanin mulkin marigayi Lamidi Adesina tsakanin 1999 zuwa 2003.

Dan uwan mamacin mai suna Adeniyi Adebisi ne ya tabbatar wa jaridar Premium Times mutuwar a daren Alhamis.

Adebisi, wanda shine kwamishinan kasuwanci da hannayen jari na jihar Oyo, ya ce: "Koleoso ya mutu a yau din nan a asibitin koyarwa na jami'ar Ibadan".

Ya kara da cewa, "Yana kokarin cika shekaru 86 ko 87 ne a duniya".

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa wani tsohon sanata rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa wani tsohon sanata rasuwa
Source: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: An sake jaddada wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da Chadi

A wani labari na daban, an ji cewa kasar Najeriya da jamhuriyar Chadi a ranar Alhamis sun amince da jaddada yarjejeniyar yakar Boko Haram da ke tsakaninsu.

Ministan tsaro, Manjo janar Bashir Magashi mai murabus ya sanar da hakan ne a taron da aka yi tsakanin hukumomin kasashen biyu a Abuja.

Ya ce yana farin cikin jaddada yarjejeniyar da ke tsakaninsu don ci gaba da tabbatar da nasarar jami'an tsaron hadin guiwa.

Ya ce kirkirar MNJTF da kasashen suka yi ya kawo babbar nasara wajen yaki da ta'addanci. Ya ce akwai bukatar su jaddada yarjejeniyar.

"Akwai bukatar mu nemi sabbin hanyoyin kawo karshen Boko Haram kuma wannan taron zai samar da amintattaun hanyoyin fatattakar ta'addancin.

"Muna bukatar sabbin tsare-tsare wajen kawo karshen ta'addanci in har muna son yankunanmu su zauna lafiya," yace.

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, mayakan Boko Haram din sun addabi yankin Arewa maso gabas din ne tun 2009.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel