Yanzu-yanzu: An samu karin masu coronavirus 14 a Najeriya, jimilla 288

Yanzu-yanzu: An samu karin masu coronavirus 14 a Najeriya, jimilla 288

Hukumar Kula da Cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar da samun karin mutane 14 da suka kamu da kwayar cutar COVID-19 wato coronavirus a kasar.

Hakan na nuna cewa jimillar wadanda suka kamu cutar a kasar ya kai 288.

A cewar hukumar ta NCDC sabbin wadanda suka kamu da cutar an samu 13 ne a jihar sai kuma guda daya a jihar Delta.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafin ta na Twitter mai lakabin @NCDCgov kamar yadda ta saba.

Kamar yadda ta bayyana a rubutun da ta wallafa a Twitter, ta ce, "misalin karfe 9.3O na ranar 9 ga watan Afrilu akwai mutum 288 da suka kamu da COVID-19 a Najeriya. Mutane 5O sun warke an sallame su yayin da mutane 7 ne suka mutu tun bullar cutar."

DUBA WANNAN: Na kama mijina yana cin amana ta har su biyu - Matar tsohon gwamnan APC

Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin kasa zagon kasa, EFCC ta ja kunnen jama'a a kan yadda wasu 'yan damfara ke tallata magungunan muguwar cutar coronavirus.

Mukaddashin shugaban EFCC, Ibrahim Magu, ya fitar da wannan takardar ne wacce Tony Orilade, mukaddashin kakakin hukumar yasa hannu.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, Magu ya ce akwai bukatar 'yan Najeriya masu kishin kasa da su kiyaye wa masu gwaji da masu bada tallafin bogi ga jama'a.

Magu ya ja kunnen jama'a masu amfani da manhajoji wadanda ba amintattu ba da su kiyaye.

Shugaban EFCC din yace, "Gwamnatin tarayya ta bayyana bayanan bankunan da ta amince a tura gudumawa. Duk wani bayanin da ya ci karo da hakan na damfara ne kuma abin gudu".

Ya kara da cewa, "Ya kamata jama'a su gano damfara a wuraren saka hannayen jari na yanar gizo wadanda suka hada da masu ninka kudi. Muna bibiyar irinsu kuma za mu kama su da masu daukar nauyinsu".

Magu ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa EFCC na sane da duk 'yan damfara da ke habaka harkokinsu sakamakon barkewar annobar coronavirus.

Ya ce hukumar za ta fallasa tare da damke duk wasu cibiyoyi da aka shirya don damfarar gumin 'yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel