Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya warke daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya warke daga Coronavirus

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyanawa duniya cewa ya samu waraka daga cutar Coronavirus bayan gwaji na biyu da aka yi masa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafin sa na Tuwita da yammacin Alhamis, 9 ga watan Afrilu, 2020.

Yace: Alhamdulillah. Yanzu na samu labarin. Gwaji na biyu da aka yi mun ya nuna cewa na warke. Ina godiya gareku gaba daya bisa addu'o'inku da goyon baya yayinda nike killace."

"Mafi muhimmi, Dukkan godiya su tabbata ga Allah mai rahama, mai jinkai."

KU KARANTA Covid-19: NCDC ta karyata batun kashe N1bn don aikewa yan Najeriya da sakonnin waya

Mun kawo muku rahoton cewa a ranar 24 ga Maris, gwamnan Bala Mohammed Kauran Bauchi, ya kamu da cutar Coronavirus.

A jawabin da mai magana da yawun gwamnan, Muhktar M Gidado ya saki, ya tabbatar da rahoton inda ya bukaci alumma su taimakawa gwamnan da addu'o'i.

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya warke daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed
Source: Facebook

A bangare guda, Olorunnimbe Mamora, karamin ministan lafiya na kasar nan yace bai san abinda ya warkar da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ba daga cutar coronavirus da ta kama shi.

A ranar Laraba ne Mamora ya bayyana hakan ga kwamiti na musamman na shugaban kasa a kan cutar, a babban birnin tarayyar Abuja.

Mamora ya ce, "Ban san yadda aka yi mai girma gwamnan jihar Oyo ya warke daga cutar coronavirus ba".

Ya ci gaba da cewa, "Ban san a asibitin da aka kaishi har ya karba magani ba. Zan so in samu bayanan don in fitar da takardar".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel