Gwamnan Arewa ya yi rabon makudan kudade ga likitoci da marasa lafiya a asibiti

Gwamnan Arewa ya yi rabon makudan kudade ga likitoci da marasa lafiya a asibiti

Marasa lafiya sun gamu da kabakin alheri yayin da gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle ya kai ziyara dubiya asibitin kwararru na Yariman Bakura dake garin Gusau a ranar Laraba.

Punch ta ruwaito gwamnan ya raba N20,000 ga kowanne mara lafiya dake kwance a asibitin, sa’annan ya baiwa likitoci da jami’an kiwon lafiya kyautar N100,000 kowannensu.

KU KARANTA: Kwana 100 da bullar Corona a duniya: Ta kashe mutane 88,981 a kasashen duniya 192

Gwamnan Arewa ya yi rabon makudan kudade ga likitoci da marasa lafiya a asibiti

Matawalle
Source: Facebook

Gwamnan ya kai ziyara asibitin ne domin duba mahaifiyar Sarkin Bungudu da aka kwantar, ya raba ma masu gadin asibitin N200,000, sa’annan ya yi ma marasa lafiya fatan samun sauki.

Bello ya yi alkawarin inganta asibitocin jahar, kuma ya yi kira ga marasa lafiyan da su dauki ciwon a matsayin kaddara daga Alllah, da fatan kuma Allah ya gafarta musu.

Haka zalika gwamnan ya zagaya asibitin inda ya duba wasu kayayyaki da gwamnatin da ta shude ta sayo, amma aka yi biris dasu a cikin sundukai ba tare da an yi amfani da su ba.

Nan take gwamnan ya bada umarnin a budesu domin fara cin gajiyarsu, kayan sun hada da gadaje masu amfani da lantarki, kujeru, katifu da sauran muhimman kayan amfanin asibiti.

A wani labarin kuma, Gwamnan jahar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nada shugaban hukumar KASCO, Bala Inuwa a matsayin sabon shugaban hukumar tattara haraji ta jahar Kano.

Hadimin gwamnan Kano a kan harkar watsa labaru, Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu, inda yace nadin ya fara aiki ne nan take.

Idan za’a tuna, tsohon shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jahar Kano, Alhaji Sani Abdulqadir Dambo ya yi murabus daga mukamin ne da kansa a ranar Laraba, 8 ga watan Afrilu.

Dambo ya bayyana haka ne cikin wata wasika da ya aike zuwa ga sakataren gwamnatin jahar Kano, inda ya ce murabus din nasa ya fara aiki ne daga ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu.

Sai dai tsohon shugaban bai bayyana wata gamsashshiyar bayani ko kakkwarar dalili game da abin da ya kai shi ga yin murabus din ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel