Kisan kiyashi: Annobar Coronavirus ta kashe likitoci 100 a kasar Italiya

Kisan kiyashi: Annobar Coronavirus ta kashe likitoci 100 a kasar Italiya

Kwararrun likitoci guda 100 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon kamuwa da suka yi da cutar Coronavirus yayin da suke kula da masu dauke da cutar a kasar Italiya.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ta ruwaito kungiyar likitocin Italiya ce ta bayyana alkalumma, inda tace an samu mutuwar ne tun daga watan Feburairu da cutar ta shiga kasar.

KU KARANTA: Kwana 100 da bullar Corona a duniya: Ta kashe mutane 88,981 a kasashen duniya 192

Kisan kiyashi: Annobar Coronavirus ta kashe likitoci 100 a kasar Italiya

Kisan kiyashi: Annobar Coronavirus ta kashe likitoci 100 a kasar Italiya
Source: UGC

“Adadin likitocin da suka mutu a sanadiyyar COVID-19 sun kai 100, wata kila ma 101 a yanzu.” Kamar yadda mai magana da yawun kungiyar FNOMCeO ya shaida ma kamfanin AFP.

Daga cikin wadannan alkalumma, har da likitocin da suka yi ritaya daga aiki, amma suka koma bakin aiki domin taimakawa wajen ceton rayukan masu dauke da cutar Corona.

Kamar yadda aka samu likitocin da suka mutu, haka zalika akwai jami’an jinya 30 ma sun mutu a sanadiyyar cutar, wanda a yanzu ta kashe mutane 11 a kasar Italy.

Shugaban kungiyar FNOMCeO, Filippo Anelli yce: “Ba zamu sake barin Likitocinmu su kula da masu cutar ba tare da sanye da kayan kariya ba, wannan ba adalci bane.”

A yau, annobar cutar Coronavirus ta cika kwanaki 100 a duniya, wanda zuwa yanzu ta sauya tsarin duniya gaba daya sakamakon yadda ta shiga duk wani lungu da sako na duniya.

A jawabinsa na cikar Coronavirus kwanaki 100 a duniya, shugaban WHO, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa:

“A yau aka cika kwanaki 100 da hukumar WHO ta samu labarin bullar cutar Corona, wanda ya fara kamar cutar ‘Nimoniya’ amma mara sababi.”

Kamfanin dillancin labaru na AFP ta ruwaito tun bayan bullar cutar a kasar China, zuwa yanzu ta kama mutane 1,519,260, ta kashe mutane 88,981, a kasahen duniya 192.

Sai dai koda yake cutar ta tafka barna saosai, amma akwai wasu mutane 312,100 suka warke daga cutar a duk fadin duniya.

Alkalumma sun nuna kasar Italiya ce kan gaba wajen yawan mace mace a dalilin cutar, inda ta kashe mutane 17,669 daga cikin mutane 139, 422 da suka kamu da cutar

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel