Coronavirus: Gwamnan Riyadh, yan gidan sarautar Saudiyya 150 sun kamu da cutar

Coronavirus: Gwamnan Riyadh, yan gidan sarautar Saudiyya 150 sun kamu da cutar

Yan gidan sarautar kasar Saudiyya akalla 150 sunkamu da cutar Coronavirus a makonni baya-bayan nan, rahotanni sun bayyana.

A cewar New York Times, gwamnan Riyadh, babbar birnin kasar Saudiyya, Yarima Faisal bin Bandar bin Abdulaziz Al Saud, mai shekaru 70 na kwance a asibiti bayan kamuwa da cutar.

Tuni Sarkin Saudiyya, Salman bin AbdulAziz, da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, sun killace kansu gudun kada su harbu da cutar.

Likitocin asibitin tunawa da Sarki Faisal dake kula da yan gidan sarauta ta shirya gadaje 500 don kula da su.

Coronavirus: Gwamnan Riyadh, yan gidan sarautar Saudiyya 150 sun kamu da cutar

Gwamnan Riyadh, yan gidan sarautar Saudiyya 150 sun kamu da cutar
Source: UGC

Asibitin ta fitar da sakon kar ta kwana ga manyan Likitocin asibitin cewa a shirya domin za a kawo wasu marasa lafiya masu uwa a gindin murhu.

Jawabin yace "Bamu san adadin mutanen da za a kawo ba amma mu kasance a shirye. A fitar da dukkan sauran marasa lafiya masu cutuka mai tsanani."

Sakon ya kara da cewa daga yanzu za a rika jinyar ma-aikatan asibitin a wani asibiti daban saboda a samu isasshen gadaje ga yan gidan sarauta.

Akwai dubunnan yarimomi a gidan sarauta kuma sukan yi tafiye-tafiye da dama kasashen Turai.

Ana kyautata zaton daga kasashen Turai suka kwaso cutar zuwa Saudiyya

Kasar Saudiyya mai adadin mutane milyan 33 ta tabbatar da mutane 2,932 sun kamu da cutar kuma 41 sun rmutu.

Ministan kiwon lafiyar kasar, Tawfiq al-Rabiah, a ranar Talata ya yi gargadin cewa da alamun kasar zata fuskanci babban kalubale cikin makonni masu zuwa.

Tawfiq al-Rabiah yace "Cikin makonni masu zuwa, bincike ya nuna cewa kimanin mutane 10,000 zuwa 200,000 zsu kamu da cutar (a saudiyya)."

Idan baku manta ba, hukumomin Masallatai biyu masu daraja sun dakatad da Sallolin Jumaa a Makkah da Madinah sai lokacin da Allah yayi saboda gudun yaduwar cutar.

Hakazalika an dakatad da ibadar Umrah kuma da yiwuwan ba za a yi Hajjin bana ba. Kasar ta umurci dukkan hukumomin jin dadin alhazan kasashen duniya su jinkirta amsan kudi hannun alummarsu tukun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel