Boko Haram: Sojojin Chadi sun bayyana adadin yan ta'addan da suka kashe

Boko Haram: Sojojin Chadi sun bayyana adadin yan ta'addan da suka kashe

A yau Alhamis ne rundunar dakarun kasar Chadi ta ce ta kammala kai hari ga mayakan Boko Haram da ke yankin iyakar Chadi da inda ta halaka 'yan ta'adda 1,000 amma sojoji 52 suka rasa rayukansu.

Mai magana da yawun rundunar, Kanal Azem Bermendoa Agouna ya sanar da AFP cewa sun yanke shawarar kai harin ne bayan rasa kusan dakaru 100 da suka yi a watan da ya gabata.

Ya kuwa kammala ne a jiya Laraba bayan sun fatattaki mayakan ta'addancin Najeriya daga kasarsu.

Ya ce, "An kashe mayakan ta'addancin dubu tare da tarwatsa kwale-kwale 50 na su".

Wannan ne karo na farko da aka samu hoton Operation Bohoma Anger, wanda aka kaddamar bayan sojojin kasar Chadi sun tafka asarar rayuka masu yawa a rana daya.

Tafkin Chadi babban waje ne da ke da ruwa inda aka samu iyakokin jamhuriyar Nijar, kasar Najeriya, Chadi da Kamaru suka hadu.

Gabar tafkin ta yammaci ne mayakan jihadin suka tsallaka daga yankin Arewa maso gabas na Najeriya. A nan ne kuma suka kaddamar da kamfen din rashin zaman lafiya tun 2009.

Boko Haram: Dakarun Chadi sun bayyana yawan mayakan ta'addancin da suka halaka
Boko Haram: Dakarun Chadi sun bayyana yawan mayakan ta'addancin da suka halaka
Asali: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: Ban san yadda aka yi Gwamna Makinde ya warke ba - Karamin Ministan Lafiya

A ranar 23 ga watan Maris, mayakan sun kai harin sa'o'i bakwai cif ga dakarun kasar Chadin a Bohoma inda suka kashe sojoji 98, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A 2015, kasashe hudu da ke da iyakoki a yankin sun hada wata rundunar jami'an tsaro ta hadin guiwa (MNJTF), wanda ya hada da jamhuriyar Benin don a yaki Boko Haram.

Amma kuma Chadi, wacce dakarunta ke da matukar karfi, sun nuna damuwarsu bayan rasa rayukan da aka yi a Bohoma.

"Chadi ce take daukar dawainiyar yakar Boko Haram," shugaban kasa Idriss Deby ya koka a ranakun karshen makon da ya gabata.

Barnar Boko Haram da ta dauka shekaru 11, ta lashe dubban rayuka a yankin Arewa maso gabas na Najeriya. Harin ya raba mutane miliyan biyu daga gidajensu a yankin.

A bangaren kasar Nijar kuwa, ma'aikatar tsaro ta Niamey ta ce rundunar sojinta tare da hadin guiwar na kasar Chadi sun kawo mummunan rashi ga mayakan Boko Haram a yankin Chadin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164