COVID-19: Obasanjo, Okonjo-Iweala sun nemi a yafe wa Afirka bashin $44bn

COVID-19: Obasanjo, Okonjo-Iweala sun nemi a yafe wa Afirka bashin $44bn

Shugabannin duniya ciki har da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo da tsohuwar manajan bankin duniya, Ngozi Okonjo Iweala sun roki kasashen mafi karfin tattalin arziki 20 na duniya G-20 su yafe wa ƙasashen Afirka bashin $44 domin basu daman yaki da COVID-19.

Mutanen biyu sun yi kira da babban murya tare da sauran shugabanni a duniya 100 na neman kasashen duniya su hada kai su dauki mataki nan take cikin yan kwanakin nan domin bawa Afirka daman yaki da COVID-19.

A cikin wasikar da suka aike wa ƙasashen na G-20, shugabannin sun ce wannan annobar ta coronavirus ta fi karyewar tattalin arzikin da duniya ta shiga daga 2008-2010, muni kamar yadda The Cable ta ruwaito.

COVID-19: Obasanjo, Okonjo-Iweala sun nemi a yafe wa Afirka bashin $44bn

COVID-19: Obasanjo, Okonjo-Iweala sun nemi a yafe wa Afirka bashin $44bn
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Na kama mijina yana cin amana ta har su biyu - Matar tsohon gwamnan APC

Wani sashi na wasikar ya ce, "A shekarar 2008 zuwa 2010,, ana iya magance matsalar tattalin arzikin da ya samu ta hanyar yin gyara a tsarin bankuna na duniya".

"Amma wannan, ba za a iya magance matsalar tattalin arzikin ba har sai an magance matsalar lafiya. Kasashen duniya ba za su koma yadda suke ba bayan an ci galaba a kan cutar har sai kuma an tabbatar dukkan kasashe sun farfado daga matsalar da COVID-19 ta jefa su ciki."

Shugabanin na Afirka sun nemi kasashen waje su yafe wa kasashe marasa karfi basusukan da ake bin su na wannan shekarar ciki har da Dalla Biliyan 44 da ake bin kasashen Afirka don su samu damar yaki da COVID19

"Muna rokon kasashen G20 su bukaci Hukumar bayar da lamuni ta duniya, IMF, da Bankin Duniya su sake duba basusukan da ake bin kasashen da annobar ta shafa," in ji su.

Shugabannin duniya da suka hada da tsaffin Farai ministan Birtaniya, Tony Blair da Gordon Brown, tsohuwar shugaban Malawi, Joyce Banda, tsohon sakataren majalisar dinkin duniya, Ban Ki Moon da wasu sun nemi a fitar da Dalla Biliyan 8 don yaki da annobar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel