Gwamnan Kano ya nada Bala Inuwa mukamin shugaban hukumar tattara haraji

Gwamnan Kano ya nada Bala Inuwa mukamin shugaban hukumar tattara haraji

Gwamnan jahar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nada shugaban hukumar KASCO, Bala Inuwa a matsayin sabon shugaban hukumar tattara haraji ta jahar Kano.

Hadimin gwamnan Kano a kan harkar watsa labaru, Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu, inda yace nadin ya fara aiki ne nan take.

KU KARANTA: Coronavirus: Yahaya Bello ya bada umarnin bude Masallatai da Coci-coci a jahar Kogi

Gwamnan Kano ya nada Bala Inuwa mukamin shugaban hukumar tattara haraji

Gwamnan Kano ya nada Bala Inuwa mukamin shugaban hukumar tattara haraji
Source: Twitter

Idan za’a tuna, tsohon shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jahar Kano, Alhaji Sani Abdulqadir Dambo ya yi murabus daga mukamin ne da kansa a ranar Laraba, 8 ga watan Afrilu.

Dambo ya bayyana haka ne cikin wata wasika da ya aike zuwa ga sakataren gwamnatin jahar Kano, inda ya ce murabus din nasa ya fara aiki ne daga ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu.

Sai dai tsohon shugaban bai bayyana wata gamsashshiyar bayani ko kakkwarar dalili game da abin da ya kai shi ga yin murabus din ba.

A wani labari kuma, yan majalisar dokokin jahar Kaduna sun sadaukar da albashinsu na watan Afrilu domin rage ma al’ummar jahar radadin halin da coronvirus ta saka su a ciki.

Mataimakin kaakakin majalisar dokokin jahar, Muktar Isah Hazo ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 8 ga watan Afrilu dake dauke da sa hannunsa.

A cikin sanarwa, Isah Hazo yace yan majalisar jahar su 34 sun yanke shawarar sadaukar da albashinsu don jama’ansu, tare da tallafa ma gwamnati a kokarin da take yi game da cutar.

Yan majalisar sun dauki wannan mataki ne domin taimaka ma kokarin da gwamnatin jahar Kaduna ke yi na bayar da tallafin kayan abinci ga gajiyayyu da marasa karfi a jahar Kaduna.

Daga karshe sanarwar ta bayyana cewa kaakakin majalisar, Yusuf Zailani ya jinjina ma yan majalisa bisa sadaukarwar da kuma halin dattaku da tausayawa da suka nuna.

Sa’annan ya yi kira ga jama’an jahar su cigaba da kauce ma shiga taron jama’a, wanke hannuwa da sauran dokoki don kiyaye kansu da kare yaduwar cutar, kamar yadda gwamnatin ta bukata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel