Annobar Coronavirus: An killace mutane 34 da suka fita yawon motsa jiki a Legas

Annobar Coronavirus: An killace mutane 34 da suka fita yawon motsa jiki a Legas

Wata kotun majistri dake zamanta a garin Yaba na jahar Legas ta kama wasu mutane 14 da laifin yin karan tsaye ga umarnin gwamnatin jahar na zama a gida don gudun yada cutar Coronavirus.

Wadannan mutane 34 sun shiga hannu ne yayin da suka taru a kan babbar titin Gbagada zuwa Oworonsoki na jahar Legas suna gudanar da atisayen motsa jiki sakamakon babu ababen hawa a kan titin saboda dokar Corona.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta mika matatun man fetir ga wata kamfani mai zaman kanta

Annobar Coronavirus: An killace mutane 34 da suka fita yawon motsa jiki a Legas
Annobar Coronavirus: An killace mutane 34 da suka fita yawon motsa jiki a Legas
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ruwaito kotun ta yanke musu hukunci bayan sun amsa tuhuma daya da ake musu na shirya gangamin da ya haura na mutane 20 kamar yadda gwamnatin jahar ta umarta.

Bayan sun amsa laifin nasu ne sai Alkalin kotun ya sanar da yanke musu hukuncin killace na tsawo kwanaki 14 a asibitin Yaba ko kuma duk wani wuri da gwamnati ta ga dama, da kuma horon aiki na kwanaki 30.

A wani labari kuma, gwamnan jahar Kogi, Yahaya Bello ya dage dokar hana bude Masallatai, coci-coci da sauran wuraren ibada domin baiwa Musulmai da sauran mabiya addinai daban daban daman gudanar da ibada kamar yadda suka saba.

Wannan umarni tana kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan watsa labaru da sadarwa na jahar, Kingsley Fanwo ya fitar a ranar Alhamis, a garin Lokoja, sai dai gwamnatin jahar ta nemi shuwagabannin addinan su tabbatar da tsare tsaren kariya daga yaduwa cutar a wuraren bautan.

Kwamishinan ya yi kira ga shuwagabannin addinai da su cigaba da gudanar da addu’o’i domin kawo ganin karshen wannan annoba ta yadda al’amuran rayuwa zasu koma yadda suke a duniya gaba daya.

Ya kara da neman shuwagabannin addinai su samar da sabulun wanke hannu na Hand sanitizer ga dukkanin mabiyansu a wuraren bauta, kuma su dabbaka tsarin zama nesa nesa da juna a wuraren bautan.

Haka zalika gwamnatin jahar Kogi ta nemi shuwagabannin addinan su dinga gajarta ibadunsu ta yadda ba zasu tara dandazon jama’a da yawa a cikin dan karamin wuri ba, wanda hakan ka iya kawo yaduwar cutar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel