A shirya nake na rattafa hannu kan sabon kwantaragi – Kocin Super Eagles

A shirya nake na rattafa hannu kan sabon kwantaragi – Kocin Super Eagles

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, Gernot Rohr ya bayyana cewa aniyarsa ta cigaba da aiki da kungiyar, don haka ya ce a shirye yake ya rattafa hannu kan sabon yarjejeniyar kwantaragin da ya shiga da hukumar kwallon kafa ta Najeriya.

Punch ta ruwaito a ranar Litinin ne shugaban NFF- hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick ya sanar da cewa sun kammala hada takardun sabon yarjejeniya a kan kwantaragin Rohr, kuma zasu aika masa zuwa mako mai zuwa.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta mika matatun man fetir ga wata kamfani mai zaman kanta

A shirya nake na rattafa hannu kan sabon kwantaragi – Kocin Super Eagles
A shirya nake na rattafa hannu kan sabon kwantaragi – Kocin Super Eagles
Asali: Getty Images

Amaju ya ce daga cikin yarjejeniyar akwai batun cewa da naira za’a dinga biyan Rohr, kuma dole ne ya samu wurin zama a Najeriya ta yadda zai dinga kallon wasannin gasar Premier ta Najeriya domin zabo zakakuran yan wasa.

Sai dai duk da wadannan sharudda, Rohr ya bayyana cewa manufarsa ita ce ya cigaba da rike Super Eagles domin ta tsallakar da su zuwa gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2021 da kuma gasar cin kofin duniya na shekarar 2023.

“Ina so na kammala aiki na a Najeriya, ina so na je gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2021 da kuma gasar cin kofin duniya, hakan na nufin dole ne mu cigaba da aiki tare.” Kamar yadda ya shaida ma tashar ESPN.

Sai dai Rohr yace karin albashin ba damuwarsa bane, baya bukatar karin kudi kowanne iri, abin da yake so kawai shi ne ya kasance an sakar masa mara, a bashi dama ya yi aikinsa yadda ya kamata ba tare da an tsoma masa baki ba, amma kafin ya rattafa hannu sai ya tattauna da mataimakansa saboda shi yake biyansu.

Daga karshe yace zama a Najeriya ba matsalarsa bane, saboda ko a shekaru uku da suka gabata ya fi zama a Najeriya fiye da zama a Turai, sai dai ya kara da cewa tunda har yawancin yan wasan Super Eagles a Turai suke taka leda ban da Ikechukwu Ezenwa, dole ne ya dinga fita a kai a kai don ganawa da su da kungiyoyinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel