Coronavirus a Najeriya: Manyan abubuwa 20 da suka faru

Coronavirus a Najeriya: Manyan abubuwa 20 da suka faru

Bisa lissafin cibiyar takaita yaduwar cuta a Najeriya NCDC ta wallafa, kawo yanzu mutane 276 suka kamu da cutar ta Coronavirus a Najeriya.

Yayinda 44 sun warke, sun samu lafiya kuma an sallamesu, 6 sun rigamu gidan gaskiya.

Jihar Legas ke kan gaba da mutane 145, sai Abuja 54, sannan Osun 20.

Ga jerin abubuwa 20 da suka faru:

1. Ranar 27 ga Febrairu 2020 aka samu bullar cutar a Najeriya.

2. Ranar 9 ga Maris shugaba Buhari ya nada kwamitin kar ta kwana na yakar cutar karkashin jagorancin Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

3. Ranar 18 ga Maris: An hana jirage daga wasu kasashe 11 shigowa Najeriya. Sun hada da Amurka, Ingila, Jamus, Norway, Sin, Dss.

4. Ranar 20 ga Maris: An kulle filayen jirgin saman Kano, Enugu, da Fatakwal.

5. Ranar 21 ga Maris: An kulle filin jirgin saman Legas da Abuja.

6. Ranar 23 ga Maris: Gwamnatin tarayya ta rufe dukkan iyakokin Najeriya na tsawon makonni hudu.

7. Ranar 24 ga Maris: Shugaban maaikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, suka kamu da cutar Coronavirus.

8. Ranar 24 ga Maris: Majalisar wakilan tarayya sun samar da dokar tallafawa yan Najeriya.

9. Ranar 24 ga Maris: An hana wasu maaikata da yan jarida da dama shiga fadar shugaban kasa.

10. Ranar 26 ga Maris: Gwamnatin tarayya ta baiwa gwamnatin Legas tukwicin bilyan goma don yakar cutar.

KU KARANTA Ba zamu baiwa Likitocin China hadin kai ba - Kungiyar Likitocin Najeriya

11. Ranar 26 ga Maris: Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana neman mutane 4,370 da sukayi mu'amala da wasu da aka tabbatar sun kamu.

12. Ranar 27 ga Maris: Shugaba Buhari ya baiwa cibiyar NCDC N15bn da suka bukata.

13. Ranar 27 ga Maris: Ministan Abuja ya bada umurnin kulle makarantun Abuja da kasuwanni.

14. Ranar 28 ga Maris: Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya kamu da cutar.

15. Ranar 29 ga Maris: Shugaba Buhari ya yi jawabi ga yan Najeriya, ya sanar da dokar rufe Abuja, Legas da Ogun na tsaon makkoni biyu.

16. Ranar 29 ga Maris: Kwantrola Janar na hukumar shiga da fice, Mohammed Babandede, ya kamu da cutar Coronavirus.

17. Ranar 30 ga Maris: Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya kamu da cutar Coronavirus.

18. Ranar 6 ga Afrilu: Buhari ya nemi bashin N2.53 Tiriliyan daga bankin duniya da IMF domin kawar da yiwuwar shiga matsin tattalin arziki.

19. Ranar 8 ga Afrilu: Gwamnatin tarayya ta kaddamar da na'urar numfashi da ruwan feshi da aka kera a Najeriya.

20. Ranar 8 ga Afrilu: Likitoci daga kasar Sin sun dira Najeriya domin taimakawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel