COVID-19: Ban san yadda aka yi Gwamna Makinde ya warke ba - Karamin Ministan Lafiya
- Karamin ministan lafiya na kasa, Olorunnimbe Mamora ya ce bai san yadda aka yi gwamna Makinde na jihar Oyo ya warke ba
- Kamar yadda yace, yana bukatar sanin inda aka killace shi da irin magungunan da ya dinga sha har ya warke daga cutar coronavirus
- A ranar 5 ga watan Afirilu ne Makinde ya wallafa cewa sakamakon gwajin cutar coronavirus din shi kashi na biyu ya bayyana, kuma ya samu waraka
Olorunnimbe Mamora, karamin ministan lafiya na kasar nan yace bai san abinda ya warkar da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ba daga cutar coronavirus da ta kama shi.
A ranar Laraba ne Mamora ya bayyana hakan ga kwamiti na musamman na shugaban kasa a kan cutar, a babban birnin tarayyar Abuja.
Mamora ya ce, "Ban san yadda aka yi mai girma gwamnan jihar Oyo ya warke daga cutar coronavirus ba".
Ya ci gaba da cewa, "Ban san a asibitin da aka kaishi har ya karba magani ba. Zan so in samu bayanan don in fitar da takardar".

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji
Mamora ya sanar da hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi a kan ko Makinde ya yi amfani da maganin gargajiya ne don samun waraka.
A ranar 5 ga watan Afirilu ne Makinde ya wallafa a shafin shi na twitter cewa ya rabu da cutar coronavirus.
Sakamakon kuwa ya bayyana ne bayan kwanaki 6 da yayi a killace kuma yana karbar magani.
A wallafar gwamnan, ya ce, "Na matukar jin dadi da addu'oinku tare da goyon bayan da na fuskanta. Ina matukar godiya. Da wannan yammacin ne na samu sakamakona na biyu da ke bayyana bana dauke da cutar".
Ya kara da cewa, "Ina matukar godiya ga Farfesa Temitope Alonge, wacce ta shugabanci kwamitin yaki da coronavirus a jihar Oyo".
Amma kuma, a taron manema labarai ne Mamora ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta shirya karbar tallafin kayan aiki da kuma kungiyar likitoci daga China don shawo kan annobar coronavirus a Najeriya.
Kamar yadda gidan talabijin na Channels ya bayyana, ya kara da cewa ministan lafiya Osagie Ehanire ne ya tarba kungiyar likitocin daga China.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng