Ba zamu baiwa Likitocin China hadin kai ba - Kungiyar Likitocin Najeriya

Ba zamu baiwa Likitocin China hadin kai ba - Kungiyar Likitocin Najeriya

- Likitoci 15 sun dira Najeriya daga kasar Sin ranar Laraba don kawo gudunmuwa

- Cikin mutane 5000 da aka yiwa gwaji a Najeriya kawo yanzu, mutane 276 suka kamu

Kungiyar Likitocin Najeriya NMA ta lashi takobin cewa mambobinta Likitoci ba zasu baiwa Likitocin kasar Sin da suka zo Najeriya hadin kai ko kadan ba. Thisday ta ruwaito.

Likitocin sun dira babbar filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja ranar Laraba domin taimakawa kasar wajen yakar cutar Coronavirus.

Kawo yanzu, mutane 276 sun kamu da cutar a Najeriya.

Shugaban kungiyar Likitocin Najeriya NMA, Francis Faduyile, yayinda yayi hira da manema labarai yace akwai sanannen ka'idar da ya kamata duk wani Likita daga kasar waje ya cika kafin iya aikin Likitanci a Najerya.

Ka'idar itace sai ya rubuta jarabawar majalisar aikin likitanci a Najeriya MDCN kuma ya lashe kafin iya aiki a Najeriya.

Ya bayyana hakan ne duk da tabbacin da gwamnatin tarayya ta bada cewa Likitocin ba aikin likitanci suka zo yi ba, innama sun zo shirya kayayyakin aiki ne da sauransu.

KU KARANTA Za mu fara kama masu yaudarar mutane da maganin coronavirus na bogi - Magu

Ba zamu baiwa Likitocin China hadin kai ba - Kungiyar Likitocin Najeriya
Ba zamu baiwa Likitocin China hadin kai ba - Kungiyar Likitocin Najeriya
Asali: UGC

Yace: “Babu abinda Likitocin kasar Sin zasu yi da zai iya qarina da abubuwan da mukeyi. Likitocin Najeriya suna iyakan kokarinsu.“

“Mun bayyana matsayarmu cewa ba mu bukatar wadannan yan Chinan a wannan lokacin.“

“Mun ji cewa ministan kiwon lafiya, Dakta OSagie Ehanire, ya ce za'a killacesu na tsawon kwanaki 14 kafin a bari su fara jinyar mutane masu cutar COVID-19.“

“Kafin su iya aikin Likitanci a Najeriya, su yi jarabawarmu. idan suka ci jarabawar, za su iya taimaka mana. Amma idan ba a yi hakan ba, babu wata alaka da zamuyi da su.“

Amma ya mika godiyarsa ga kasar Sin kan kayayyakin kiwon lafiya da suka kawo wa Najeriya na gudunmuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel