Na kama mijina yana cin amana ta har su biyu - Matar tsohon gwamnan APC

Na kama mijina yana cin amana ta har su biyu - Matar tsohon gwamnan APC

- Florence Ajimobi, uwargidan tsohon gwamnan jihar Oyo ta ce sau biyu tana kama mijinta yana cin amanarta amma tana yafe mishi

- Florence dai ta yi wannan bayanin ne a hirar kai tsaye da tayi da diyarta mai suna Bisola ta kafar sada zumuntar zamani ta Instagram

- Ta ce duk macen da ke ji da kanta, ta gwada bibiyar mijinta. Ragowarta ne kuma zai dawo mata ko bayan ya kwanta da wata

Florence Ajimobi, uwargidan tsohon gwamnan jihar Oyo, ta ce ta kama mijinta yana cin amanarta har sau biyu amma ta yafe mishi.

Uwargidan tsohon gwamnan ta bayyana hakan ne a wata tattaunawar kai tsaye a Instagram da tayi da diyarta mai suna Bisola, yayin da take bayanin kalubalen da ta fuskanta a aurenta da tsohon gwamnan.

Na kama mijina yana cin amana ta har su biyu - Matar tsohon gwamnan APC
Na kama mijina yana cin amana ta har su biyu - Matar tsohon gwamnan APC
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Florence ta kwatanta Ajimobi da "ragowarta" wanda dole ya dawo gareta.

DUBA WANNAN: An sako shahararren dan wasan kwallon kafa Ronaldinho daga gidan yari

Ta kara da cewa maza na cin amanar matansu ne kawai ta hanyar kwanciya da matan banzan amma ba wai don kauna ba.

"A lokutan da na kama shi yana cin amanata, yana bani hakuri. Idan kuma ya bada hakuri, toh ya wuce don bana kara komawa kan laifin. Bana kuma tattaunawa da shi a kai," tace.

"Ana laifi kuma ana yafiya a duk zaman tare. Ko a matsayina na matarshi, wani lokacin ina yin abinda bai dace ba, kuma wasu abubuwan sun fi cin amana zafi," a cewar ta.

"Na san wasu matan da ke gina gidaje ba tare da sanin mijinsu ba. Wannan mummunan abu ne. Wasu na killace kazaman sirrikansu daga mazansu. Wani lokacin, na kan yi laifin da bana iya kallonshi," in ji ta.

Na kan tura mishi sako, ba saboda bana son ganin fuskar shi ba. Ina tura mishi sako kuma yayi min martani, hakan ya wadatar, ta ce.

Ta kara da kalubalantar 'yan matan da ke ji da kyan su da su gwada bibiyar mijinta. Ta ce zai yi amfani dasu ne kawai yayi watsi dasu daga bisani.

"Na lamushe inda za a mora a tare dashi", matar tsohon gwamnan tace.

"A tunanina, maza da yawa na cin amana ne don su kwanta da mace ba wai don suna sonta ba. A lokacin kuwa da namiji ya kwanta da matar da yake so, yana soyayya ne ba wai kwanciya ba," Florence tace.

"Idan kina alfahari da kyan ki, ki gwada mijina. Nawa ne ni kadai. Zai yi amfani da ke ne ya kuma yi watsi tare da dawowa gareni. Ragowata ne, na lamushe inda yafi amfani nashi," A cewar Florence.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164