Gwamnatin Buhari za ta mika matatun man fetir ga wata kamfani mai zaman kanta

Gwamnatin Buhari za ta mika matatun man fetir ga wata kamfani mai zaman kanta

Shugaban hukumar man fetir ta Najeriya, NNPC, Mele Kyari ya bayyana cewa daga yanzu NNPC za ta cire hannunta daga gudanar da matatun man fetir na kasa gaba daya.

Premium Times ta ruwaito Kyari ya bayyana haka ne cikin wani hira da yayi da gidan talabijin na Arise a ranar Laraba, kamar yadda kaakakin hukumar, Kennie Obateru ya bayyana.

KU KARANTA: Annobar Corona: Shugaban kasa ya dakatar da minista saboda karya dokar hana zirga zirga

Gwamnatin Buhari za ta mika matatun man fetir ga wata kamfani mai zaman kanta
Gwamnatin Buhari za ta mika matatun man fetir ga wata kamfani mai zaman kanta
Asali: UGC

Kyari yace daga yanzu gwamnati za ta mika aikin gudanarwar matatun man Najeriya g wata kamfani mai zaman kanta, wanda za ta kula da ayyukansu da kuma kulawa da su, amma sai an kammala garambawul da ake musu.

Tun daga shekarar 1999 ake antaya biliyoyin kudade a matatun man fetir na Najeriya, amma hat yanzu babu daya daga cikinsu dake aiki dari bisa dari, sai Kyari na ganin wannan sabon tsarin da suka bullo da shi zai haifar da Da mai ido.

“Za mu bayar da kwangilar gudanar da matatun man Najeriya, NNPC za ta cire hannunta, zamu samu kamfanin dake da tabbacin za ta iya gudanar dasu na wani lokaci, burinmu mu sauya salon tafiyar da su don ganin sun yi aiki.” Inji shi.

Ya kara da cewa daga karshe suna fatan kamfanonin masu hannun jari za su shigo a dama dasu wajen tafiyar da matatun man Najeriya kamar yadda aka yi ma NLNG, inda masu hannun jari ne ke yanke shawarar abin da ya kamata, yace yana ganin hakan zai kawo sauyi a matatun mai ma.

Bugu da kari Kyari ya kara da cewa yana sa ran za’a kammala aikin gyaran matatun man Najeriya zuwa shekarar 2022, aikin da aka fara tun a watan Janairun bana.

Game da karyewar farashin gangar danyen mai kuwa, Kyari ya ce akwai haske a gaba, sakamakon ana sayar da gangar mai $15 a makon da ta gabata, amma a wannan makon ta kai $32.79, don haka yace idan aka cigaba da tattaunawa da kasashe masu arzikin mai, komai zai daidaita zuwa karshen shekara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel