Yanzu-yanzu: An samu sabbin mutum 22 da suka kamu da Coronavirus a Najeriya

Yanzu-yanzu: An samu sabbin mutum 22 da suka kamu da Coronavirus a Najeriya

Hukumar Kula da Cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar da samun karin mutane 22 da suka kamu da kwayar cutar COVID-19 a kasar.

Hakan na nuna cewa jimillar wadanda suka kamu cutar a kasar ya kai 276.

A cewar hukumar ta NCDC sabbin wadanda suka kamu da cutar an samu 15 ne a Legas, hudu a birnin tarayya Abuja, biyu a jihar Bauchi, sai kuma guda daya a jihar Edo.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafin ta na Twitter mai lakabin @NCDCgov kamar yadda ta saba.

DUBA WANNAN: Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji

A wani rahoton, kun ji cewa a ranar Alhamis 9 ga watan Maris ne gwamnatin tarayya za ta fara sakin fursunonin da shugaban Buhari ya yi wa afuwa ta musamman a yunkurin ta na rage cinkoso a gidajen na gyaran hali a kasar.

Jaridar Leadership ta gano cewa za a fara sakin fursunonin ne bayan amincewar shugaban kasa Buhari da bukatar da ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya gabatar masa don rake cinkoso a gidajen yarin.

Gwamnatin tarayyar ta Najeriya ta dauki wannan matakin ne don rage yaduwar kwayar cutar coronavirus a kasar.

Wannan sakon na cikin wata takardar gayyata ne da ofishin ministan ta aike wa manema labarai na gayyatar su taro a hedkwatan hukumar kula da gidajen gyaran hali na kasa, NCoS.

Kakakin hukumar da NCoS, DCC A.C. Njoku ne ya saka hannu a kan sakon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel