COVID-19: NECO ta karyata rade-radin cewa za ta dage jarrabawar BECE da SSCE

COVID-19: NECO ta karyata rade-radin cewa za ta dage jarrabawar BECE da SSCE

- Hukumar Jarabawa ta Kasa (NECO) ta musanta labarin dage jarabawoyin daliban aji uku da na aji shida na sakandire

- Kamar yadda shugaban fannin yada labaran hukumar ya sanar, suna lura da halin da kasar ke ciki ne kafin daukar mataki

- Hukumar ta bayyana cewa ta dage jarabawar masu kammala karatun firamare don shiga sakandire ta shekarar 2020

Hukumar jarabawa ta kasa (NECO) ta musanta rade-radin dage jarabawoyinta da ake yadawa sakamakon barkewar annobar coronavirus a kasar nan.

A wata takarda da shugaban fannin yada labarai da hulda da jama'a, Malam Azeez Sani ya fitar, ya ce hukumar ta bayyana cewa jarabawar masu kammala firamare kadai ta dage.

Ya ce labarin dage jarabawoyin da suke yawo a kafafen sada zumuntar zamanin duk na bogi ne kuma ba gaskiya bane.

COVID-19: NECO ta yi bayani a kan rade-radin dage jarabawar NCEE da SSCE

COVID-19: NECO ta yi bayani a kan rade-radin dage jarabawar NCEE da SSCE
Source: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: An gano 'yan Najeriya 5 a China dauke da kwayar cutar

Ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da labaran marasa tushe balle makama.

Ya ce, "Hukumar ta duba sauran jarabawoyin masu kammala aji uku da kuma aji shida na sakandare amma tana tantamar dagesu a halin yanzu."

Ya kara da cewa, "Ana kira ga daukacin jama'a da su yi watsi da labaran bogin don hukumar na lura da abinda ke faruwa a kasar nan, kuma za ta sanar da matsayarta idan da bukatar hakan."

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa NECO ta dage rubuta jarabawar kammala firamare na 2020 a ranar 24 ga watan Maris.

"NECO na sanar da masu rubuta jarabawa, iyaye da kuma masu ruwa da tsaki cewa ta dage jarabawar NCEE har sai yadda hali yayi," A cewar takardar.

"Wannan hukuncin ya biyo bayan kokarin gwamnatocin tarayya da na jihohi ne wajen ganin an shawo kan barkewar cutar coronavirus a kasar nan, in ji hukumar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel