COVID-19: An gano 'yan Najeriya 5 a China dauke da kwayar cutar

COVID-19: An gano 'yan Najeriya 5 a China dauke da kwayar cutar

- 'Yan Najeriya biyar ne aka gano sun kamu da cutar coronavirus a kasar China

- Kamar yadda rahotanni daga kasar suka nuna, sun samu cutar ne daga wani gidan cin abinci da suka kai ziyara ba sau daya ba

- An gano cewa mai gidan abincin da ke yankin Guangzhou tare da yaranta na dauke da cutar

'Yan Najeriya biyar ne suka kamu da cutar coronavirus a kasar China, jaridar Daily Mail ta ruwaito.

Hudu daga cikinsu sun ziyarci "Emma Food", wani gidan cin abinci ne kamar yadda hukumar kiwon lafiya ta Guangzhou ta sanar.

Mamallakiyar gidan cin abincin, diyarta da wani dan ta duk an gano suna dauke da muguwar cutar.

An gano cewa 'yan Najeriyan na dauke da muguwar cutar ne daga ranar 28 ga watan Maris zuwa 30 ga wata. Hakan ta faru ne bayan tantance matafiya 3,779 da kasar tayi.

COVID-19: An gano 'yan Najeriya 5 a China dauke da kwayar cutar
COVID-19: An gano 'yan Najeriya 5 a China dauke da kwayar cutar
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An sako shahararren dan wasan kwallon kafa Ronaldinho daga gidan yari

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, cutar ta fara ne daga garin Wuhan na kasar China din inda ta lashe rayukan jama'a masu tarin yawa.

Garin Guangzhou na nan a kilomita 1,028 daga kudancin tsakiyar garin.

Yankin Yuexiu, inda gidan cin abincin yake an saka mishi tsauraran matakai sakamakon gano tarin masu cutar da aka yi a ciki.

Lamarin kuwa ya tada hankulan jama'a ne don an gano mutane 466 masu dauke da cutar.

Mutane 197 ne da suka mu'amalanci masu cutar kuma an killacesu don yi musu gwaji.

Mai gidan cin abincin Emma mai suna Zhuang, an killace ta ne tun a ranar 1 ga watan Afirilu.

Diyarta mai shekaru 8 tare da kawarta duk an gano suna dauke da muguwar cutar washegarin gano cewa mahaifiyarsu na dauke da ita.

Tuni dai aka rufe gidan cin abincin sannan za a bincike shi.

An kara da rufe dukkan gidajen cin abincin yankin na kwanaki 14, kafafen yada labarai na kasar China suka ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel