Da duminsa: Buhari ya rage kasafin kudin 2020, ya tura majalisa

Da duminsa: Buhari ya rage kasafin kudin 2020, ya tura majalisa

Gwamnatin tarayya ta aika sabon kasafin kudin tarayya majalisar dokokin tarayya domin sake dubawa saboda halin da kasa ke ciki na annobar cutar Coronavirus da fadin farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Kasafin kudin da Buhari ya tura kamar yadda wasu alkaluma suka bayyana ya ragu daga N10.594 trillion zuwa N10.276 trillion.

Hakazalika an rage kiyasin farashin danyen mai a kasuwar duniya daga $57 zuwa $30 kuma an rage adadin gangar man da za a rika haka a rana daga gana milyan 2.7 zuwa gangan 1.7.

Bugu da kari, an kara farashin dalar Amurka daga N305 zuwa N360.

Za ku tuna cewa bayan alaka ta shekara da shekaru tsakanin kasar Rasha da Saudiyya kan farashin danyen man fetur a kasuwar duniya, an samu sabani kuma hakan ya shafi dukkan sauran kasashe masu arzikin man fetur.

A cewar rahoton The Economist, mambobin kungiyar kasashe masu fitar da man fetur wato OPEC, sun yi kokarin yin yarjejeniya kan adadin danyen man da za'a rika fitarwa.

Amma a ranar Juma'a, 6 da Maris, maimakon yarjejeniyar da aka bukaci yi, an yi baran-baran a ganawar saboda kasar Rasha ta ki amincewa da rage adadin man feturin da zata rika fitarwa kuma hakan bai yiwa Saudiyya dadi ba.

Ba tare da bata lokaci ba kasar Saudiyya ta karya farashin man feturin da kimanin kashi 30%.

A ranar Juma'a da aka kammala ganawar, farashin gangar man fetur a kasuwar duniya ta fado daga $50 zuwa $45, amma a ranar Litinin, ta fado warwas zuwa $31.

Da duminsa: Buhari ya rage kasafin kudin 2020, ya tura majalisa

Da duminsa: Buhari ya rage kasafin kudin 2020, ya tura majalisa
Source: Twitter

KU KARANTA Duk da mutuwar mutum daya makamakon Coronavirus, gwamnatin Katsina ta janye dokar hana Sallar Juma'a

A bangare guda, Najeriya za ta samu wasu kudi masu yawa daga babban bankin Duniya domin bunkasa sha’anin lafiya. An soma ba Najeriya wannan kudi da nufin habaka harkar kiwon lafiyar kasar.

A wani jawabi da bankin ya fitar a Ranar Talata, 7 ga Watan Afrilu, 2020, an ba Najeriya fam Dala miliyan 82 ta wani shiri na REDISSE da aka kawo domin inganta harkar kiwon lafiya.

Hukumomi sun nemi alfarmar bankin ya kawowa Najeriya agajita yadda za a gyara asibitoci cikin watanni shida. Bankin ya bayyana wannan a babban birnin tarayya da ke Abuja.

Ana kyautata zaton za a yi amfani da wadannan kudi da sun haura Naira Biliyan 29 wajen gyara asibitocin gwamnati a yanzu da Najeriya ta ke ta fama da annobar cutar Coronavirus.

“Bada gudunmuwa ga hanyoyin samun abincin jama’a da kuma taimakawa kananan ayyukan na samun abin kashewa a cikin shekaru biyun nan zai taimaka wajen rage radadin tattali.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel