COVID-19: An gurfanar da mutum 17 a kan karya dokar takaita zirga-zirga

COVID-19: An gurfanar da mutum 17 a kan karya dokar takaita zirga-zirga

A ranar Laraba ne 'yan sanda a jihar Legas suka gurfanar da wasu karin mutane 17 wadanda suka take dokar zaman gida ta gwamnatin jihar.

Wadanda aka gurfanar din kamar yadda jaridar The Nation Online ta bayyana, sune: Adekunle Peter mai shekaru 28, Rilwan Babajide mai shekaru 18, Bukola Oyekola mai shekaru 30, Kennedy Ubogu mai shekaru 30, Yusufa Lawal mai shekaru 25, Saheed Isiaka mai shekaru 24, Olamide Wasiu mai shekaru 17, Wisdom Edokpayi mai shekaru 34 da kuma Michael Duyilemi mai shekaru 34.

Sauran sun hada da Francis Ofen mai shekaru 20, Babatunde Mukaila mai shekaru 19, Sunday Nwanga mai shekaru 28, Chukwuma Ifeadi mai shekaru 30, Kareem Akeem mai shekaru 23, Chibuzor Okonkwo mai shekaru 40, Zakariyu Mohammed mai shekaru 29, Olasunkanmi Akanbi mai shekaru 37 da kuma Babatunde Oalfusi mai shekaru 40.

COVID-19: An gurfanar da mutum 17 a kan karya dokar takaita zirga-zirga
COVID-19: An gurfanar da mutum 17 a kan karya dokar takaita zirga-zirga
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Covid19: Yadda mutane suka yi wawaso wurin rabon tallafin kayan abinci a Kaduna

Masu kare kansu din sun bayyana ne a gaban wata kotun majistare da ke Yaba a kan zarginsu da ake da yin taro da kuma caca.

Gwamnati ta haramta walwala ga mazauna garin tare da basu umarnin zaman gida in har ba aiki na musamman ake yi ko bukata ba.

An yi hakan ne kuwa don shawo kan yaduwar muguwar cutar coronavirus.

Wadanda aka gurfanar din duk sun amsa laifukansu.

Kungiyar masu gabatar da kara wacce ta samu jagorancin Cyril Ejiofor na hukumar binciken laifuka na jihar Legas da ke Yaba, ta sanar da kotun cewa sun aikata laifin ne a ranar 1 ga watan Afirilu a Ajegunle.

Kungiyar ta kara da bayyana cewa wadanda aka gurfanar din sun take dokar zaman gida ta jihar kuma an kama su da laifin yin caca.

Alkalin kotun, Peter Ojo, ya yanke musu hukuncin aikin taimakon anguwa na wata daya cif.

Za su dinga yi ne a babbar kotun jihar Legas din daga karfe 9 na safe zuwa 3 na yamma a kowacce rana.

Ya ce, "Za su tabbatar da sun tsaftace ciki da wajen ofisoshin. Ba a yanke hukuncin don nishadi ba amma sai don zaman lafiya da kuma walwalar jama'a."

"Babbar barazana ga jama'a ce cutar nan kuma basu dauke ta a bakin komai ba. Abun alhini ne," ya kara da cewa.

Ojo ya kara da cewa a killacesu na kwanaki 14 a cibiyar killace majinyatan cutuka masu yaduwa da ke Yaba. Ya kuma tilasta cewa a yi musu gwajin muguwar cutar coronavirus.

Ya ce duk kuwa wanda aka gano yana dauke da cutar zai fara shan magani.

"Idan har wadanda ake kara basu dauke da cutar, a hanzarta miko su don karbar hukuncinsu," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel