Shirin ko-ta-kwana: Ana ci gaba da ginin cibiyar killace masu cutar coronavirus a Kano

Shirin ko-ta-kwana: Ana ci gaba da ginin cibiyar killace masu cutar coronavirus a Kano

A wani kokari na shirin ko-ta-kwana da gwamnatin jahar Kano ke yi, ta dukufa gadan-gadan wajen ganin ta yi duk wani tanadi da ya kamata a kan cutar coronavirus, wacce a yanzu ta karade wasu jihohin kasar.

A yanzu haka mun samu labarin cewa, ana nan ana ci gaba da aikin gina cibiyar killace masu cutar ta coronavirus wacce mai kudin Afrika Alhaji Aliko Dangote tare da hadin gwiwar gwamntin ta jahar Kano suka dauki nauyinta.

Ana wannan aiki ne a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a cikin birnin Kano.

Shirin ko-ta-kwana: Ana ci gaba da ginin cibiyar killace masu cutar coronavirus a Kano

Shirin ko-ta-kwana: Ana ci gaba da ginin cibiyar killace masu cutar coronavirus a Kano
Source: Twitter

Zuwa yanzu dai hukumomi ba su bayar da sanarwar bullar cutar ba a Jahar Kano amma ta bulla makobciyarta wato Kaduna, inda mutane biyar suka kamu.

A yanzu haka dai jimlar mutane 254 ne suka harbu da cutar a Najeriya, kamar yadda hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta fitar a bayananta.

Shirin ko-ta-kwana: Ana ci gaba da ginin cibiyar killace masu cutar coronavirus a Kano

Shirin ko-ta-kwana: Ana ci gaba da ginin cibiyar killace masu cutar coronavirus a Kano
Source: Twitter

Daga cikin wannan adadi, mutane 44 sun warke sannan shida sun rasa rayukansu.

A gefe guda mun ji cewa gwamnatin jahar Kano ta karawa ma'aikatanta hutun zama a gida na tsason wasu sati biyun domin dakile yaduwar cutar covid-19 a jahar.

Dakta Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jahar Kano, ne ya sanar da hakan yayin da ya karbi rahoton kwamitin wucin gadi da ya kafa domin neman tallafin kudi. Ya ce karin wa'adin hutun yana daga cikin shawarar da gwamnatinsa ta yanke a matsayin rigakafin kare jama'a daga kamuwa da cutar covid-19 a jihar.

"Akwai fargaba har yanzu, saboda har yanzu yawan masu kamuwa da kwayar cutar da wadanda cutar ta kashe karuwa yake yi a Najeriya," a cewar Ganduje.

Bayan karbar rahoton kwamitin, gwamna Ganduje ya jinjinawa mambobin kwamitin tare da yabawa aikin da suke yi. Kazalika, ya basu tabbacin cewa nan bada dadewa ba za a raba tallafin da aka samu ga mabukata.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin kuma shugaban jami'ar Bayero ta Kano, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, ya sanar da gwamnan cewa yanzu haka akwai tsabar kudi miliyan N364.6 a asusun banki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel