Annobar Corona: Shugaban kasa ya dakatar da minista saboda karya dokar hana zirga zirga

Annobar Corona: Shugaban kasa ya dakatar da minista saboda karya dokar hana zirga zirga

Shugaban kasar Afirka ta kudu, Mista Cyril Ramaphosa ya dakatar da ministar sadarwa, Stella Ndabeni Abrahams, na tsawon watanni 2 sakamakon kamata da aka yi da laifin karya dokar hana shige da fice da zirga zirga a yayin marran annobar Coronavirus.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito fadar shugabank kasar Afirka ta kudu ta bayyana daga cikin watanni biyu da shugaba Ramaphosa ta dakatar da Stella, ba za’a biyata albashin wata daya ba.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Yan majalisun Kaduna sun bayar da makudan kudade don taimaka ma jama’a

Mai magana da yawun shugaba Ramaphosa, Khusela Diko ta bayyana cewa: “Game da zargin

Annobar Corona: Shugaban kasa ya dakatar da minista saboda karya dokar hana zirga zirga
Annobar Corona: Shugaban kasa ya dakatar da minista saboda karya dokar hana zirga zirga
Asali: UGC

da ake yi ma minista cewa ta yi ma dokar hana zirga zirga karan tsaye kuwa, gwamnati ta yanke shawarar kyale doka ta yi aikinta a kan ta.”

Musabbabin wannan hukunci shi ne cece kucen da jama’a suka yi game da cewa an hangi minista Stella a gidan wata kawarta inda ta je cin abinci, wanda karara hakan ya saba ma dokar hana shige da fice da shugaban kasar ya sanya don kare yaduwar Coronavirus a kasar.

Wannan ne tasa shugaban ya gayyaci Minsitar zuwa fadar shugaban kasa a ranar Laraba, inda ya nuna mata bacin ransa bisa abin da ta aikata, duk da cewa Stella ta nemi gafara, kuma shugaban ya amsa, amma ya bayyana rashin gamsuwarsa da hujjojin da ta bayar.

Don haka shugaban ya caccaki ministar, sa’annan ya umarceta ta nemi gafarar al’ummar kasar Afirka ta kudu, bugu da kari ya umarci Minista Jackson Mthembu ya maye gurbinta har zuwa lokacin da za ta kammala wa’adinta.

A yanzu haka dai kasar Afirka ta kudu tana da mutane 1,749 dake dauke da cutar, kuma ta kashe mutane 13 yayin da mutane 95 suka warke. Sai dai gwamnatin kasar ta kama akalla mutane 20,000 da laifin karya dokar ta baci.

A wani labarin kuma, yan haya da dama a kasar Kenya za su samu sauki yayin da kungiyar masu gidajen haya da yan haya ta kasar, LATAK, ta yafe musu kudin hayan watanni uku sakamakon bullar annobar Corona virus mai toshe numfashi a kasar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng