COVID-19: An killace mutane 27 a jihar Neja

COVID-19: An killace mutane 27 a jihar Neja

- Gwamnatin jihar Neja ta killace mutane 27 bayan an zargesu da mu'amala da wani mutum mai dauke da cutar coronavirus

- Mazauna kauyen Makira da ke jihar ne suka sanar da aukuwar lamarin ga hukumomi bayan mutumin ya nuna alamun cutar

- Bayan zuwansu kauyen don daukar mai cutar, ya bi wata motar kasuwa inda yayin yunkurin barin kauyen tare da wasu fasinjoji

Gwamnatin jihar Neja ta killace mutane 27 bayan an zargesu da mu'amala da wani mutum mai dauke da cutar coronavirus.

Mutumin ya iso ne daga karamar hukumar Mashegu ta jihar Legas, gidan talabijin din Channel ya ruwaito.

Kamar yadda shugaban kwamitin shugaban kasa a kan cutar coronavirus kuma sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Matane yace, mazauna kauyen Makira a jihar ne suka sanar da aukuwar lamarin.

A ranar Litinin ne mazauna kauyen suka sanar da hukumomi cewa akwai wani mutum wanda yake nuna alamomin cutar coronavirus.

Ya ce kwamitin ya gaggauta isa kauyen inda aka gano mutumin. Ya jaddada cewa wanda ake zargin, ya nemi tserewa ta hanyar hayewa wata motar kasuwa.

COVID-19: An killace mutane 27 a jihar Neja
COVID-19: An killace mutane 27 a jihar Neja
Asali: UGC

KU KARANTA: Mamaki da al'ajabi: Buhari ya bayyana na hannun daman Jonathan a matsayin dan takarar sanatan APC

A yayin karin bayani, sakataren gwamnatin ya bayyana cewa kwamitin shugaban kasar, tare da jami'an tsaro ne suka samu nasarar tare motar kasuwar tare da kwaceta kacokan.

Ya kara da cewa an killace dukkan fasinjojin da ke ciki tare da wanda ake zargin yana dauke da cutar saboda kusancin da suka samu.

A halin yanzu, kwamishinan lafiya na jihar, Dr Mohammed Makusidi ya ce an dauka jininsu kuma an kai Abuja don gwaji.

Ya ce a yayin da suke killace a cibiyar killace masu dauke da cutuka masu yaduwa a Minna, gwamnatin jihar za ta tabbatar da cewa an dauka dawainiyarsu yadda ya dace har da ciyarwa.

Mutanen kuwa da ke jibge a cikin motar kasuwar da wanda ake zargi da kamuwa da cutar sun kai 26. Hade da mutumin ne suka cika 27.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel